Mai tantabaru da katafariyar tukunyar jollof a hotunan Afirka na mako

Asalin hoton, FEISAL OMAR / REUTERS

Bayanan hoto, A birnin Mogadishu na kasar Somalia, matashi Zakaria Mohamed mai shekara 17 a duniya na kula da tantabaru a unguwar da yake zama, kamar yadda ya saba.
    • Marubuci, Natasha Booty
  • Lokacin karatu: Minti 3

Zababbun hotuna masu kayatarwa da aka dauko a fadin Afirka da ma tsallake:

Asalin hoton, OLYMPIA DE MAISMONT / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ranar Asabar a birnin Legas da ke Najeriya, ‘yar shekara 23 Toni Olaguniu ta caba ado a matsayin wata jarumar bidiyo game

Asalin hoton, OLYMPIA DE MAISMONT / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Shi ma Toby Adekunle ya yi tasa shigar a matsayin daya daga cikin jaruman bidiyo game din League of Legends a birnin Ikko

Asalin hoton, EMMANUEL ADEGBOYE / EPA

Bayanan hoto, Taron da aka yi ya tattaro masoya litattafan raha da fim din ‘yar tsana da bidiyo game da finafinai a birane daban-daban na duniya

Asalin hoton, APTN

Bayanan hoto, A ranar Juma’ar makon da ya gabata shahararriyar mai girke-girke Hilda Baci ta dora hamshakiyar tukunyarta a kan murhu domin kafa tarihin girka shinkafa dafa-duka mafi yawa a duniya, inda ta kai nauyin kusan tan 9.

Asalin hoton, TERESA SUAREZ / EPA

Bayanan hoto, A birnin Paris na Faransa, wadannan matan ‘yan asalin Ivory Coast suna hada abincin kasarsu, daga cikin sama da mutanen kasashe 60 da suka fafata.

Asalin hoton, ANTONIN THUILLIER / AFP

Bayanan hoto, Bayan kafa sabon tarihi a gudun tsallake shingaye na tazarar mita 3000 a Japan, da alama ‘yar Habasha Sembo Almayew na neman hutu nan take

Asalin hoton, JEWEL SAMAD / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Haka nan ma a gasar wasan tsalle-tsalle ta duniya a ranar Asabar, Beatrice Chebet ta Kenya ta ciri tuta a gasar tseren tazarar mita 10,000.

Asalin hoton, AMOS GUMULIRA / AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Magoya bayan jam’iyyar MCP mai mulkin Malawi sanye da kayan jam’iyyar sa’ilin wani gangamin yakin neman zabe a ranar Asabar. Har zuwa ranar Alhamis ba a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar ba amma duk da haka na kusa da shugaban kasar da kuma jagoran adawa duk sun yi ikirarin samun nasara.

Asalin hoton, BEN WHITLEY / PA Wire

Bayanan hoto, ‘Yar Najeriya mai zane-zane da rajin kare muhalli Nnenna Okoreon ta yi baje-kolin aikinta a lambun Kew Gardens da ke birnin Landan ranar Alhamis.

Asalin hoton, ROCCO SPAZIANI / MONDADORI PORTFOLIO / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Asabar ‘yar kasar Benin Angélique Kidjo ta halarci wani taro a Vatican.