Waɗanne hanyoyi Trump zai iya bi don yi wa Zohran Mamdani ƙafar ungulu?

New York

Asalin hoton, Getty/Reuters

Lokacin karatu: Minti 4

Jim kaɗan bayan da Zohran Mamdani ya lashe zaɓen Magajin Garin birnin New York, Ya mayar da hankalinsa kan gawagwarmayarsa ta gaba: karawa da shugaban ƙasar Amurka.

A jawabinsa bayan samun nasara, da ya gabatar a ranar Talata, Mamdani ya juya kan kyamarori don yin magana kai tsaye ga Donald Trump, "tunda na san ka na kallo, ina da da kalomomi hudu a gare ka, ka ƙara sautin Talabijin ɗinka."

Shugaba Donald Trump ya soki matashin mai shekaru 34 a duniya, yana mai cewar yana wakilitar masu ra'ayin gurguzu, wanda kuma ita ce makomar jam'iyyar Democrats.

Trump ya mara wa tsohon gwamna na jam’iyyar Democrat Andrew Cuomo baya, wanda ya shiga takara a matsayin dan takara mai zaman kansa, sannan ya yi barazana ga al'ummar New York cewar zai daina bai wa birnin kuɗi. Washegarin ranar da Mamdani ya samu nasara, Trump ya gargadi mutane da su "tsere" daga New York.

Wannan shi ne karon farko ba da Trump wanda aka haife shi a New York, ya yi yunƙurin yin katsa landan a harkokin tafiyar da birnin.

Tun bayan dawowa kan mulki, Trump ya yi amfani da ikon da yake da shi na gwamnatin tarayya a kan biranen da ‘yan jam’iyyar Dimokrats ke mulki, ya aike da dakarun taron ƙasa tare da ƙaddamar da wani tsattsauran kamen ƴan ci rani a faɗin Amurka.

Ya kuma yanke biliyoyin daloli daga kuɗaɗen biranen, tun bayan tsayawar ayyukan gwamnati a 1 ga watan Oktoba, ciki har da birnin New York, inda ya rufe asusu, dala biliyan 18 daga kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke ba su, don amfani da su a ɓangaren gine-gine.

Masana harkokin siyasa sun shaida wa BBC cewar, Trump zai iya rage kashe kuɗaɗe, wanda hakan zai iya zama cikas ga alƙawarin da Mamdani ya yi a wajen yaƙin neman zaɓen sa na rage tsadar rayuwa.

Mamdani, wanda ya bayyana kansa a matsayin "Dan gurguzun Democrat" ya yi kira a lokacin da yake yaƙin neman zaɓen sa cewar zai samar da sufurin motar safa mai sauƙi da sauri, da samar da rukunin gidaje masu sauƙin farashi, da tsarin lafiya na bai ɗaya, da shagunan sayar da kaya masu rahusa, da sauran manufofi da za su kawo ci gaba.

Giɓin da za a samu na kuɗin da gwamnati za ta tura na dala biliyan 8

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana harkokin siyasa sun ce Mamdani, wanda tsohon wakili ne a majalisar dokokin New York, ya fuskanci ƙalubale daban-daban fiye da Trump, wajen cimma burinsa na siyasa.

Ya bayana cewar za iya tara kudin shiga da ya kai dala biliyan 10, ta hanyar ƙara haraji kan kamfanoni masu kaurin jari, ta hanyar yin ƙarin da kashi daya, kan masu albashi mai tsoka a New York, amma sai dai duka sai ya samu amincewar gwamna.

Kawo yanzu, gwamna Kathy Hochul, da ke fuskantar ƙalubale mai tsanani a zaɓen baɗi mai zuwa, ta yi jinkirin nuna goyan bayan ta ga tsarin harajin na Mamdani. Elise Stefanik makusanciyar Trump, ta sanar da cewar za ta nemi yin takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar Republican.

Trump ya ce zai iya ƙirƙirar giɓi a nan gaba idan shirinsa na ƙara rage kuɗin da gwamnatin tarayya ke bayarwa, da ya kai dala biliyan 8.5 a shekarar da ta gabata, ya kai wajen kashi 7 da kasafin kuɗin jihar.

Zelizer ya ce, Za a iya samun mastaloli na kuɗi, da za su iya kawo cikas, ga ayyukan da ake yi a birnin. Kuma idan kudaden da gwamnatin tarayyar ke baya wa suka fara yin ƙasa, abu ne mai wuya a iya aiwatar da sabbin manfofin.

Magoya bayan Mamdani na da yaƙinin cewar shi ne ɗan takarar da ya fi mayar da hankali  wajen kawo saƙin rayuwa a birnin

Asalin hoton, Getty Images

Waɗannan kuɗaɗe ana amfani da su ne a kan ayyuka daban-daban, ciki har da sashen samar da gidaje, da ayyukan gaggawa, da na kula da lafaiyar yara, da shirin tallafin abinci na ƴan makaranta da suka fito daga gidajen ƙananan ma'aikata, a cewar ofishin kula da kasafin kuɗin binin na New York.

Sai dai trump bai sanar da takamaimai wane kudin gwamnatin tarayyar zai rage din ba.

Sarah Parker, wata bababr mai bincike ce da tsar-tsare ta ofishin kasafin kudi na birnin New York da ke zaman kansa, ta ce doka ta bai wa birnin damar samar da wasu daga cikin abubuwan more rayuwar, da suka haɗa da samar da tsarin muhalli ga wadanda da ba su da shi. Hakan na nufin cewar rashin kuɗaɗen daga gwamnatin tarayyar, tilas gwamnatin birni ta ɗauki wasu matakai na daban, ta hanyar matsa lamba a wasu daga cikin shirye-shiryenta.

A ɓanagren Justin de Benedictis-Kessner, Farfesa mai fashin baƙi kan manufofin gwamnati a jami'ar Havard, ya ce trump na iya fuskantar turjiya ta hanyar ƙalubalantar sa ta fuskar kotu, idan har ya rike kudaden da majalisar ta amince da su, ciki har da na tallafin abinci.

"Sai dai hakan zai kawo tsaiko wajen samun kuɗin, zuwa ga al'ummar da ke buƙatarsa," a cewar sa.

Aikawa da Dakarun tsaro na ƙasa

Isowar dakarun tsaro na ƙasa birnin Los Angeles, da ya janyo zanga-zanga a birnin

Asalin hoton, Getty Images

Trump ya kuma yi barazanar amfani da jami'an tsaro kan biranen da ƴan jam’iyyar Dimokrats ke mulki. Ya aika da dakarun ƙasa na tsaro zuwa birane masu yawa ciki har da irin su Los Angeles, da Portland, da Oregon, da Washington, D.C., ya na mai bayyana su da biranen da ake fama da aikata manyan lafiuka, da ke buƙatar a kakkaɓe su, saboda buƙatar tallafin gwamnati wajen ɗaukar mataki a kan lamarin.

Sai dai ya dakata da aikawa da dakaru zuwa babban birnin Amurka, sai dai masana harkokin siyasa sun ce hakan ka iya sauyawa.

Zelizer, ya ce "ya gama tsara abin da ya ke son ya yi. Abu ne mai wuya, ka ga hakan ba ta faru ba."

Mamdani ya nanata cewar mayar da hankali wajen ƙalubalantar al'amura ta fuskar shari'a, a martaninsa ga aikawa da dakarun tsaron kasa zuwa New York, kamar yadda sauran biranen suka yi. Wasu daga cikin waɗannan shari'o'in na gaban kotu.