Buƙata shida da ta sa ma'aikatan jinya shiga yajin aiki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Laraba ne dai ma'aikatan jinyar na Najeriya suka fara yajin aikin gargaɗi na mako guda a faɗin ƙasar, ƙarƙashin ƙungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya.
Yajin aikin zai kuma shafi asibitocin tarayya da sauran cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya kaɗai.
Wannan yajin aikin na zuwa ne bayan da ƙungiyar ta bai wa gwamnati wa'adin kwanaki 15 domin magance matsalolin da ke damun su.
A wata wasiƙa da Sakatare Janar na ƙungiyar, Dr. Shettima, ya sa wa hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa sun bai wa ma'aikatar lafiya ta tarayya wa'adin kwanaki 15 domin cika bukatunsu.
"Bayan tattaunawa mai zurfi da mambobin kwamitin NEC dangane da matsalolin da muke fuskanta, ƙungiyar ta yanke shawarar bai wa ma'aikatar Lafiya wa'adin kwanaki 15 domin cika buƙatun da muka gabatar," in ji Dr. Shettima.
An saka ranar fara yajin aikin ne a ranar Litinin 14 ga Yuli, 2025, amma daga baya aka fara shi a ranar Laraba 30 ga Yuli, 2025.
Ƙorafi shida da ma'aikatan jinya da ungozoma ke yi
A cewar kafafen yaɗa labarai na cikin gida, ƙungiyar ta lissafo buƙatun da ma'aikatanta ke neman gwamnati ta cika musu kamar haka.
- Duba kuɗin alawus-alawus na aiki da dare da kuma ta gyara shi.
- Ƙara kuɗin alawus na kayan sawarsu.
- Samar da tsarin albashi na musamman domin ma'aikatan jinya kawai.
- Kara alawus na ƙarin ayyukan da suke yi bacin ainihin aikinsu.
- Gwamnati ta ɗauki ma'aikatan jinya da yawa aiki domin rage karancin ma'aikata.
- Gwamnati ta buɗe sashen ma'aikatan jinya a Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya domin kula da buƙatun aikin jinya kai tsaye.
A cewar jaridar Punch, Shugaban Kungiyar ma'aikatan jinya na FHI, Malam Morakinyo Rilwan, ya ce:
"Har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe mu ba kan wannan batu. Shi ya sa muke cewa yajin aikin dole ne ya ci gaba, kuma babu abin da zai dakatar da shi.
"Ko da gwamnati ta kira mu yau ko gobe, hakan ba zai hana yajin aikin ba," in ji shi.
Ya ce gwamnati ba ta nuna damuwa da walwalar jama'a ba, shi ya sa suka bari kwanaki 15 suka wuce ba tare da ɗaukar mataki ba.
"Fiye da shekaru 40 kenan muna hakuri da su. An bar mu muna aiki ba tare da kayan kariya irin su gloves ko kayan aiki ba, kuma cikin sama da shekaru 40, ba mu taba shiga yajin aiki ba sai yanzu," Rilwan ya ƙara da cewa.
Asibitocin da ba sa yajin aiki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban Kungiyar ma'aikatan jinya na FHI, Malam Morakinyo Rilwan ya ce dukkanin mambobinsu sun amince da shiga yajin aikin idan banda Federal Medical Centre, Ebute-Metta da ke Lagos da asibitin koyarwa Lagos.
Ya ce jami'ansu a asibitocin biyu ba su shiga yajin aikin ba saboda sun janye daga ƙungiyar tun kimanin shekaru uku da suka wuce saboda wasu saɓani.
A Najeriya, yajin aikin ma'aikatan kiwon lafiya abu ne da ake yawan fuskanta, saboda yadda sassa daban-daban na fannin kiwon lafiya ke ci gaba da buƙatar gwamnati ta gyara halin da ake ciki.
A karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ministan kiwon lafiya, farfesa Mohammed Ali Pate, ya taɓa fada wa BBC a wata hira da aka yi da shi a Oktoba 2024, cewa gwamnati ta yi alƙawarin magance duk wata matsala da ma'aikatar kiwon lafiya ke fuskanta kuma za ta yi ƙoƙarin hana yajin aiki, kuma yawan yajin aikin ma'aikatan lafiya ya ragu.
Amma abin mamakin shi ne, ƙasa da shekara guda bayan wannan alƙawari, wani sabon yajin aiki ya sake kunno kai.











