Milan ta kammala ɗaukar Gimenez daga Feyenoord

Santiago Gimenez

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

AC Milan ta kammala ɗaukar ɗan wasan tawagar Mexico, Santiago Gimenez daga Feyenoord kan yarjejeniyar kaka huɗu da rabi, kamar yadda ta sanar ranar Litinin.

Gimenez ya koma Feyenoord a Yulin 2022 kan yarjejeniyar kaka huɗu, wanda ya ci ƙwallo 65 a wasa 105 a babbar gasar tamaula ta Netherlands.

Wasu rahotanni daga Italiya na cewa Milan ta biya $32.78 million kudin ɗan wasan mai shekara 23, wanda ya buga wa Mexico karawa 32 da cin ƙwallo huɗu.

Gimenez shi ne na biyu da ya je Milan a Janairun nan, bayan da ta ɗauki aron Kyle Walker daga Manchester City.

Gimenez wanda ya zura ƙwallo 16 a raga a wasa 19 a bana, zai saka riga mai lamba bakwai, wadda Alvaro Morata ya yi amfani da ita.

Ranar Lahadi Motara ya koma Galatasaray, wadda zai yi wa wasannin karo kan yarjejeniyar kaka ɗaya.

Milan ta tashi 1-1 da Inter Milan a San Siro ranar Lahadi a Serie A, hakan ya sa tana ta takwas a kan teburin babbar gasar tamaula ta Italiya ta kakar nan.

Ranar Laraba Milan za ta fafata da Roma a zagayen kwata fainals a Coppa Italia.