Chelsea ta kammala ɗaukar Neto daga Wolverhampton

Pedro Neto

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta kammala sayen ɗan wasan Wolverhampton Wanderers, Pedro Neto kan £54m.

Mai shekara 24 ya saka hannu kan kwantiragin kaka bakwai da ƙungiyar Stamford Bridge da za ta kare a karshen 2031.

An gabatar da ɗan wasan tawagar Portugal a gaban magoya baya ranar Lahadi a lokacin da aka yi hutu a wasan sada zumunta tsakanin Chelsea da Inter Milan.

Tun ranar Juma'a Chelsea ta kulla yarjejeniyar sayen ɗan wasan, bayan da ƙungiyar Molinuex ta ƙi sallama tayi biyu da aka fara yi wa ɗan ƙwallon.

Chelsea za ta biya £51.3m ƙudin Neto da karin £2.6m na tsarabe-tsarabe.

Neto, ya koma Wolves daga Lazio a 2019, wanda ya ci mata ƙwallo14 a wasa135 a ƙungiyar da ke buga Premier League.

Wannan shi ne ciniki mai tsada da Wolves ta yi wajen sayar da ɗan wasa, wanda ya haura £47m da ta sayar da Ruben Neves ga Al-Hilal ta Saudi Arabia.

Kawo yanzu Chelsea ta kashe £185m, wajen sayen ƴan ƙwallo kan fara kakar bana.

Cikinsu har da Kiernan Dewsbury-Hall da Renato Veiga da Omari Kellyman da Filip Jorgensen da Tosin Adarabioyo.

Sauran sun haɗa da Aaron Anselmino da Caleb Wiley da Estevao Willian da kuma Marc Guiu.

Haka kuma Chelsea na fatan sayen ɗan wasan Atletico Madrid, Samu Omorodion da mai tsaron ragar Genk, Mike Penders a kwanaki masu zuwa.