Ramadan 2025: Yaya ake gane ketowar alfijir da faɗuwar rana?

Asalin hoton, Getty Images
Ketowar alfijir da faɗuwar rana, abubuwa ne muhimmai dangane da azumi, la'akari da cewa ana daina ci ko sha ko mu'amalar iyali ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana.
To sai dai mutane da dama suna samun kansu cikin shakku game da waɗannan lokuta.
Wannan dalilin ne ya sa muka tattauna da malaman addini domin ƙarin bayani kan abin da addini ya ce dangane da waɗannan lokuta.
Ya ake gane ketowar alfijir?

Asalin hoton, Getty Images
Salihu Muhammad Yakub, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya , kuma mamba a kwamitin ganin wata na mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, ya ce tantance ketowar alfijir abu ne mai wahala, musamman ga mazauna birane da manyan alƙaryu, saboda manyan gine-ginen da ke biranen.
Sheikh Salihu Yakub ya ce yadda suke yi a kwamitin shi ne sukan fita wajen gari inda babu gine-gine da yawan bishiyoyi, domin tantance ainihin lokacin da alfijir din ke ketowa, inda suke amfani da lokacin wajen tsara kalandun da ake amfani da su a masallatan ƙasar.
Ya kuma ƙara da cewa ''alfijir wani siririn haske ne da ke ketowa ta inda rana ke fitowa, za ka ganshi ya kama daga arewa zuwa kudu a kwance, musamman idan kana fili fetal'', in ji shi.
Ya ake gane faɗuwar rana?

Asalin hoton, Getty Images
Dangane da faɗuwar rana, malamin Jami'ar ya ce ita rana fahimtar faɗuwarta na da sauƙi fiye da gane ketowar alfijir.
''Ai ita rana galibi, ana ganin ta kuma in ba a lokacin damina ba, za ka ga lokacin da take faɗuwa, saɓanin ketowar alfijir'', in ji ɗan kwamitin ganin watan.
Ya ƙara da cewa daga ka daina ganin ranar, to shi kenan rana ta faɗi kenan.
''Ai shi ya sa ma kake ganin ba a fiye samun rikici a sallar magariba ba'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ƙara da cewa saboda abu ne da yake a fili , wanda ba ka buƙatar wani ya gaya maka, koda kuwa a birni kake.
Za a iya amfani da lokacin agogo ko na kalanda?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh Salihu Yakub ya ce ai a yanzu lokacin agogo da kalandu su ne ma kan gaba wajen gane lokaci a manyan biranen duniya.
Wani babban Malami mai suna, Muhammad bin Abdurrahman Aljuzairi ya rubuta wani littafi da a ciki yake cewa ana gane lokutan sallah ne - ciki akwai ketowar alfijir - ta hanyoyi guda biyar - 'Assa'at, alfalakiya, almunzabida, almabniyya, wal hisabissahih', wato wadanna kalandu ko digital agogo da ake amfani da su.
Malamin ya ce kalandun da ake sanyawa a cikin masallatar da agogunan da ake sanyawa da aka saita da lokaci sahihi.
Malamin ya ce ko a Najeriya ma kwamitinsu na ganin wata ne yake fitar da irin waɗannan kalandu, kuma sai da suka yi lissafi mai inganci kafin su zauna su fitar da lokutan sallah ciki kuwa har da ketowar alfijir.
''Don haka muke bayar da shawarar amfani da waɗanann kalandu, musamman ga mazauna birane, saboda mun bibiye su na tsawon shekara guda kafin muka fitar da su, domin amfani,'' a cewar malamin jami'ar.
Me ake nufi da 'jinkirta sahur da gaggauta buɗe baki'?

Asalin hoton, Getty Images
Akwai hadisin Manzon Allah (S.A.W) da yake cewa ''Mutane ba za su gushe ba suna cikin alkairi, muddin suna jinkirta sahur, suna kuma gaggauta buɗe baki''.
Malamin jami'ar ya ce sunna ce mai ƙarfi amfani da koyarwar hadisin, musamman la'akari da ƙwaɗaitarwar da ya yi wa al'ummar musulmi na samun alkairi.
''Abin da Hadisin ke nufi shi ne da zarar rana ta faɗi, an daina ganin ta to shi kenan lokacin shan ruwa ya yi, sai a sha ruwa'', in ji shi.
Amma dangane da sahur malamin ya ce abin da hadisin ke nufi shi ne a jinkirta shi har zuwa kusa da ketowar alfijir.
''Alal misali kamar a ce yau alfijir zai keto da misalin ƙarfe 5:40am to za ka iya cin abinci har zuwa 5:35am'', a cewar malamin.
Ya ƙara da cewa ba a so kuma mutum ya yi sakaci ya kai har daidai lokacin fitowar ko ma ya zarta.
''An tambayi wani sahabi zuwa wane lokaci kuke tsayar da sahur dinku, sai ya amsa da cewa tsakani da ketowar alfijir gwargwadon yadda za ka iya karanta aya 50'', to ga ka ai wannan ba zai wuce minti biyar ko bakwai ba,'' in ji ɗan kwamitin ganin watan.











