An kama masu tarzoma 1,500 da suka 'kai wa majalisar Brazil harin ta'addanci'

Supporters of ex-leader Jair Bolsonaro were taken by buses to a local police station

Asalin hoton, Reuters

Hukumomin kasar Brazil sun kama kimanin mutum 1,500 bayan da magoya bayan tsohon Shugaba Jair Bolsonaro suka kutsa ginin majalisar kasar da fadar shugaban kasa da kuma kotun kolin kasar.

 Tarzomar ta barke ne mako guda bayan da aka rantsar da Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva.

 Shugaban ya yi tir da abin da ya kira "ayyukan ta'addanci" kuma ya kuduri aniyar hukunta masu tarzomar.

 Sai dai tsohon shugaba Bolsonaro, wanda bai amsa cewa ya sha kaye a babban zaben ba, ya tafi Amurka daf da a mika mulki. kuma a halin yanzu yana jinya a wani asibiti da ke Jihar Florida, inda aka ce yana fama da ciwon ciki.

 Sabon Shugaba Lula tare da shugabannin majalisar kasar da na kotun koli - duka sun yi tir da "ayyukan ta'addanci da na yunkurin juyin mulki da barnata dukiyar kasa" da suka auku yayin tarzomar.

 Tarzomar ta tilastawa Shugaba Lula kaddamar da aiki da dokar ta baci a fadin kasar.

Bolsonaro supporters vandalising the interior of the presidential palace

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda magoya bayan Mista Bolsonaro suka rika lalata wasu bangarori na Fadar Shugaban Brzail

A ranar Litinin hukumomi suka kama mutum 1,200 baya ga wasu 300 da aka kama tun ranar Lahadi.

Ministan Shari'a na kasar, Flavio Dino ya sanar cewa jami'an tsaro sun kuma kwace wasu motocin bas 40 da masu tarzomar suka yi amfani da su domin isa wuraren da suka aikata laifukan.

Mista Bolsonaro ya ce bai goyi bayan hare-haren da magoya bayan nasa ke kai wa ba, amma sai bayan sa'a shida da aukuwar lamarin sannan ya wallafa sakon nasa a shafinsa na Twitter.

A sanadiyyar tarzomar, Kotun Kolin Brazil ta sauke gwamnan Jihar Brasilia, Ibaneis Rocha na tsawon kwana 90 saboda "gazawarsa wajen hana aukuwar tarzomar da kuma kin cewa komai kan batun".

Mista Rocha ya nemi afuwan 'yan kasar kan rawar da ya taka.