Abin da masu amfani da soshiyal midiya za su ƙaurace wa lokacin azumi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
A cikin shekara goma da ta gabata, duniya ta samu sauye sauye musamman a fannin fasaha, kuma a halin yanzu wannan ci gaba ya sanya mafi yawan mutane a duniya suna da wayar hannu ta zamani da ake shiga kafafen intanet.
A duniyarmu ta yau, amfani da kafafen sada zumunta ya zamo wani ɓangare na rayuwar yau da kullum.
Waɗannan shafuka na sada zumunta sun zamo hanyar da muke gudanar da harkoki da dama na rayuwa kuma yanayin amfanin da muke da su yana shafar rayuwarmu.
Saboda tasirin waɗannan shafuka a rayuwarmu, akwai buƙatar tantance yadda ya kamata a yi amfani da su a lokacin azumin Ramadan domin kaucewa saɓa wa Allah.
Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya, malamin addinin musulunci ne a jihar Kano kuma a hirarsa da BBC ya bayyana hanyoyin da ya kamata musulmi su yi amfani da soshiyal mediya a lokacin da ake cikin azumin Ramadan.
Shehin malamin ya ce ma'anar azumi ita ce kamewa daga duk wani abu da zai iya jefa mutum cikin zunubi da saɓon Allah.
"Ko da mutumin ya kasance yana kamewa kafin azumi, to ya ƙara yin haka a lokacin azumi ka da ya faɗa ciki fitina ko musiba ko kuma bala'i," in ji Gadon Kaya.
Cikin abubuwan da malamin ya ce musulmi su ƙauracewa lokacin azumi sun haɗa da:
- Kallon kaɗe-kaɗe da raye-raye
- Kallon tsiraici na mata
- Yin maganganu marasa amfani
- Yaɗa wa da wallafa bayanai da ba su da tushe
- Kallon fina-finai da hotuna na banza
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh Abdullahi Gadon Kaya ya ce "abin takaici ne idan ka je YouTube ka ga abubuwan da ake yi babu daɗi, musulmi mai azumi bai kamata ya ga wannan ba.
"Abubuwan da ake yi a TikTok sai dai kawai mu ce Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, wasu abubuwan ma idan ka gani sai ya karya maka azumi," in ji Malamin.
Ya ce ya kamata masu azumi su ɗauke hannunsu daga kan TikTok, Instagram da kuma YouTube idan ba abin da zai amfane su a kan addini ba, idan kuma suna so azumin ya kai lami lafiya wajen Allah SWT.
Sheikh Abdullahi ya ce azumi lokaci ne na kame baki, kunne, ido, hanci, gaba, kuma ana kame ci da sha da mu'amaloli na haram.
"Yanzu Alhamdulilah malamai suna ƙoƙari. A duka waɗannan shafuka, akwai wa'azuka da karatukan Al-Kur'ani da salloli da tarawi da tahajjud da kuma tafsirai a dukkan yaruka, malamai na yi ana ɗora wa a faɗin duniya don a canza wa mutane daga kallon wancan ɓarna su dawo suna ganin alkhairi," in ji Sheikh Abdullahi Gadon Kaya.
Ya ce in musulmi za su kalli TikTok su kalli wa'azuka, su kuma tabbatar da cewa duk in da za su shiga su kalli abu na alkhairi ba na sharri ba.
"Idan an yi waɗannan abubuwa za su taimaka wajen kulawa da kuma tsare mutuncin azumi," in ji Malamin.
Abin da za a yi don samun ƙarin lada a soshiyal midiya lokacin azumi

Asalin hoton, Abdullahi Gadon Kaya/FB
Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya ya ce waɗannan shafukan sadarwa na zamani suna cin lokaci ta hanyar hana musulmi karatun Al-Kur'ani, yin zikiri da kuma jin wa'azi.
A don haka ya ce akwai abubuwan da suka kamata musulmi su yi ko su yaɗa lokacin azumi domin samun ƙarin lada a watan na alfarma.
Cikin abubuwan da malamin ya ce musulmi su yawaita yi lokacin azumi sun kunshi:
- Yaɗa tafsirai: Ya ce duk inda aka yi tafsirai mutane su yaɗa shi zuwa ga sauran musulmi.
- Yaɗa karatun Al-Kur'ani: Ya ce musulmi su yawaita tura ƴan uwansu karatu ko shafukan Al-Kur'ani mai girma.
- Kallon abubuwan alkhairi
- Isar da sakonni da musulmi za su ƙaru da su lokacin azumi
Malamin addinin musuluncin da ke jihar Kano ya ce su ma kafofin yaɗa labarai suna da ta su gudummawa da za su bayar a lokacin azumi musamman ta hanyar kiran malamai su ba da jawabi ko fatawa kan abubuwan da ke karya azumi da ƙarawa azumi lada, faɗar falalar yin sallar tarawihi da tahajjudi, da kuma shirye-shirye kan muhimmancin ciyarwa da taimakon gajiyayyu.
Ya kuma ce ya kamata a zaburar da gwamnati su saukaka wa mutane da hanyoyin da ƴan kasuwa za su inganta kasuwancinsu a sauƙaƙa wa talakawa, da kuma yin kira ga masu kuɗi wajen ganin sun taimaka wa mabuƙata da sauransu.











