Dalili biyar da ya sa tattalin arzikin China ke cikin matsala

chinese feeding in the street

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cutar korona ta tagayyara China, kasa ta 2 mafi girman tattalin arziki a duniya

Daga Suranjana Tewari

Wakiliyar kasuwanci a Asiya

------------------------

Tattalin arzikin China na tafiyar hawainiya yayin da take daidaita kokarin kakkabe annobar korona da kuma raguwar bukatun sayen kaya a duniya.

Nan gaba kadan ne, ake sa ran fitowar alkaluman hukuma kan bunkasar tattalin arziki na watan Yuli zuwa Satumba - idan tattalin arzikin na kasa ta biyu mafi girma a duniya ya samu komada, hakan zai kara yiwuwar samun karayar tattalin arzikin duniya.

Burin mahukuntan Beijing - na samun bunkasar kashi 5.5% a shekara - a yanzu ya subuce duk da yake hukumomi suna shashantar da bukatar lallai sai an cimma burin.

Da kyar China ta kauce wa komada a watan Afrilu zuwa Yunin bana. A wannan shekara, wasu masana tattalin arziki ba su yi tsammanin samun wata bunkasa ba. Kasar mai yiwuwa ne ba ta fama da gagarumin hauhawar farashi kamar Amurka da Burtaniya, amma tana da wasu matsaloli - masana'antu a fadin duniya kwatsam na samun masu sayen kaya kalilan a cikin gida da kuma a ketare.

Hatsaniyar kasuwanci tsakanin China da kasashe masu ci gaban masana'antu kamar Amurka, tana dakile bunkasar. Darajar kudin China yuan ta kama hanyar faduwa warwas da ba ta taba yin irinta ba cikin shekaru gommai daidai lokacin da take sauka kasa idan an kwatanta da dalar Amurka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kudi mai raunin daraja yana razana masu zuba jari, abin da ke rura wutar rashin tabbas a kasuwannin hada-hadar kudi. Haka kuma zai sa da wuya babban bankin kasar ya iya zuba karin kudi hannun jama'a.

Duk wannan na faruwa ne a lokacin da al'amura suka kara zafi ga Shugaba Xi Jinping - yana sa ran samun wa'adin mulki na uku karon farko a tarihin kasar yayin babban taron Jam'iyyar Kwamunisanci da za a fara ranar 16 ga watan Oktoba.

To, takamaimai a ina matsalar take?

1. Kokarin kakkabe cutar korona na haifar da mummunan sakamako

Barkewar korona a birane daban-daban ciki har da matattarar masana'antu kamar Shenzhen da Tianjin, tana illa ga harkokin tattalin arziki a masana'antu. Mutane kuma ba sa kashe kudi a kan abubuwa kamar abinci da lemuka da kayan masarufi ko zuwa yawon bude ido, abin da ya sa muhimman ayyuka cikin matsi.

A bangaren masana'atu, harkokin kamfanoni ga alama sun sake habaka a watan Satumba, a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasar. Mai yiwuwa an samu farfadowar ne saboda gwamnati ta kara zuba kudi a harkokin ababen more rayuwa.

Sai dai hakan na zuwa ne bayan an shafe wata biyu ba tare da samun bunkasa a masana'antu ba. Lamarin ya janyo tambayoyi musamman tun bayan wani bincike da ya nuna cewa harkokin kamfanoni tabbas sun yi kasa a watan Satumba, inda bukatun sayen kaya suka zarce abin da ake samarwa da sabbin odar kaya da aikin yi.Bukatar sayen kaya a kasashe kamar Amurka ta ragu saboda karin kudin ruwa da hauhawar farashi da yakin Ukraine.

Kakkabe annobar korona na yi wa China illa. Kwararru sun amince cewa gwamnati na iya kara azama don zaburar da tattalin arzkin kasar, sai dai dalilan da za su sa a yi hakan kadan ne, matukar ba a ga karshen korona ba.

"Babu dumbin amfanin zuba kudi cikin harkokin tattalin arzikinmu idan harkokin kasuwanci ba za su iya bunkasa ko mutane ba za su iya kashe kudi ba," in ji Louis Kuijs, babban masanin tattalin arzikin Asiya a Cibiyar S&P Global Ratings.

2. Abin da hukumomin Beijing ke yi bai isa ba

Hukumomin Beijing sun shigo cikin lamarin - a watan Agusta sun sanar da shirin zuba yuan tirliyan 1 ($203bn) don habaka kananan sana'o'i da ababen more rayuwa da harkar gina gidaje. Sai dai jami'ai na iya bin karin dumbin matakai don zaburar da mutane su kashe kudi, ta yadda za a cimma burin bunkasa da kirkiro ayyukan yi.

President Xi waving a hand

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Xi ne da kansa ya matsa lambar bullo da dabarun kakkabe korona

Wannan ya hadar da zuba karin kudi cikin harkar samar da ababen more rayuwa da sassauta sharuddan ba da bashi ga masu sayen gidaje da harkar gidaje da harkokin kananan hukumomi da jingine wa magidanta biyan haraji. "Martanin gwamnati ga raunin tattalin arzikin dai matsakaici ne kwarai idan an kwatanta da abin da muka gani a baya lokacin da tattalin arziki ya yi rauni," a cewar Mista Loius Kuijs

3. Kasuwar samar da gidajen China ta auka cikin matsala

Raunin harkoki a bangaren samar da gidaje da bahaguwar fahimta a cikin harka babu ko tantama sun dakushe samun bunkasa. Hakan ya yi matukar nakasa tattalin arziki saboda harkar gidaje da sauran masana'antu da ke tallafa mata, cimma fiye da kashi daya cikin uku na arzikin da China ke samu a cikin gida.

"Lokacin da gwiwa ta yi sanyi a kasuwar samar da gidaje, hakan zai sa mutane su kasa samun tabbaci game da daukacin harkokin tattalin arziki," in ji Louis. Masu sayen gidaje suna kin biyan rancen da suka karba na gine-ginen da ba a kammala ba, kuma wasu sun auka cikin wasu-wasin anya ma za a taba kammala gininsu kuwa.

Bukatun sayen sabbin gidaje sun ragu, hakan kuma ya tauye bukatar shigar da kayan da ake amfani da su wajen gine-gine. Duk da kokarin gwamnatin Beijing na zaburar da harkokin gina gidaje, farashin gidaje a gomman birane ya karye da fiye da kashi 20% a bana. Yayin da masu harkar gina gidaje suka shiga cikin matsi, masharhanta sun ce hukumomi na iya kara zage damtse wajen dawo da kwarin gwiwa a kasuwar samar da gidaje.

4. Sauyin yanayi yana ta'azzara lamurra

Matsanancin yanayi ya fara illar da za a shafe dogon lokaci ana fama da ita a harkar masana'antun China. Tsananin zafi, wanda fari ya biyo baya sun auka wa lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar da birnin Chongqing da ke tsakiyar China a watan Agusta. Yayin da bukatun sayen na'urar sanyaya gida suka karu, hakan na zuke karfin lantarki a yankin da kusan kacokam ya dogara a kan lantarkin da ake samu daga kafofin ruwa.

An tilasta wa kamfanoni ciki har da manyan masana'antu kamar Foxconn da Tesla masu yin wayar iPhone zaftare sa'o'in aiki ko rufe harkokinsu gaba daya. Hukumar kididdiga ta China ta ce a Agusta ribar da ake samu a masana'antun mulmula tama da karafa ta ragu da fiye da kashi 80% a cikin wata bakwai na farkon 2022, idan an kwatanta da irin wannan lokaci a bara. Hukumomin Beijing daga bisani sun kawo dauki ta hanyar zuba biliyoyin daloli don tallafa wa kamfanonin makamashi da manoma.

5. Hamshakan kamfanonin kere-kere na China suna rasa masu zuba jari

Wata dirar mikiya da hukumomin tabbatar da bin doka suka yi wa hamshakan kamfanonin kasar - wanda tuni ya shiga shekara ta biyu - ba ya taimakawa. Tencent da Alibaba sun ba da rahoton samun raguwar kudin shiga karon farko a wata hudun baya-bayan nan - ribar kamfanin Tencent ta fadi da 50%, yayin da tsagwaron ribar da kamfanin Alibaba ya samu, ta ragu da rabi.

China's real estate market

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matsalar da harkar gina gidajen China ke ciki ta yi tsananin da ke nakasa bunkasar tattalin arziki

Dubban matasan ma'aikata ne suka rasa ayyuka - abin da ya ta'azzara matsalar rashin aikin yi, inda duk 1 cikin mutum 5 na 'yan shekara 16 zuwa 24 ke fama da rashin aikin yi.

Hakan kuma za ta iya yin illa ga zafin aikin kamfanonin China da bunkasar tattalin arziki a dogon lokaci mai zuwa.

Masu zuba jari na jin cewa hukumomin Beijing na kokarin sauya alkibla- ana kara bin diddigi kan harkokin wasu kamfanonin 'yan kasuwa masu gagarumar nasara, yayin da kokarin rukunkume ikon Shugaba Xi ke karuwa.

Daidai lokacin da kamfanoni mallakar gwamnati ga alama suka fi samun alfarma, masu zuba jari daga ketare na kwashe kudadensu.

Katafaren Bankin Softbank na Japan ya kwashe makudan kudade daga kamfanin Alibaba, yayin da kamfanin Berkshire Hathaway na Warren Buffet yake sayar da hannayen jarinsa a kamfanin BYD mai kera motocin lantarki.

An kwashe jarin fiye da $7bn daga kamfanin Tencent a kashi na biyu na wannan shekarar kadai. Amurka kuma na yin dirar mikiya kan kamfanonin China da suka bude harkoki a kasuwar hannayen jarin Amurka.

"Ana ta dage wasu shawarwarin zuba jari, kuma wasu kamfanonin ketare naneman fadada harkoki a wasu kasashen," kamar yadda Cibiyar S&P Global Ratings ta ce a wani bayani da ta fitar a baya-bayan nan.

Duniya ta fara sabawa da gaskiyar cewa China ba lallai ne ta ci gaba da bude kofofinta don harkokin kasuwanci kamar yadda ta yi a baya ba - yayin da Shugaba Xi ke fuskantar kasadar sullubewar nasarar tattalin arzikin da bunkasa China a 'yan shekaru gommai.