Sojoji sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Najeriya da wasu 'yan bindiga a Nijar.

Jirgin sama

Asalin hoton, Nigeriaairforce

Bayanan hoto, Jirgin saman yaki na Nijeriya

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta kai hare-haren ne kan tarin ‘yan ta’adda a wani kebabben wuri da ake kira Tagaushe a tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno

Ta ce al'amarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Nuwamba a garin Tagaushe.

Kakakin rundunar sojin Sama na Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya shaida wa BBC cewa hoton bidiyo ya nuna cewa ‘yan ta’addan da yawansu ya zarce 100 na taruwa a wurin domin su gudanar da wani taro ko shirya yadda za su kai wani babban hari:

“An gansu sun taru a wuri guda, akwai gidaje kamar guda uku ko hudu, ba mu san abinda ya kai su wurin ba, ko sun je su yi taro ne ko sun je su yi shaye- shayensu ne ba bu wanda ya sani, amma su na rike da bindigogi kuma akwai manyan motocinsu guda uku kuma sun cika a ciki”

“Da aka kewaye aka duba cewa za su iya kai kari sa aka jefa bam kuma an kashe da dama daga cikinsu”, In ji shi.

Rundunar sojin sama wadda ta kai hare -haren karkashin shirin Operation hadarin daji ta ce hare haren sun rutsa da wasu manyan kwamandojin Boko Haram

“An Kashe Abu Asad wanda ke aiki tare da Ali Ngulde wanda jigo ne a kungiyar Boko Haram bangaren Shekau. Akwai wasu manyan 'yan ta’adda da suka hada da Ibrahim Nakeeb da Mujaheed Dimtu da Mustafa Munzir da sauran mayaka da dama da aka kashe a hare haren ta sama” in ji shi.

Air Comodore Gabkwet ya danganta nasarar da sojojin kasar su ke samu wajan karya lagwon mayakan Boko Haram kan makaman zamani da gwamnatin Najeriya ta samar wa sojojin kasar

Sai dai ya ce akwai bukatar ganin cewa gwamnatin tarraya ta gudanar da bincike a kan yadda mayakan Boko Haram ke samun kudi tare da sayan makamai da manyan motoci da kuma yadda suke daukar matasa.

A makobciyya Jamhuriyar Nijar rundunar sojin kasar ita ma ta sanar da kashe mahara hudu a farmakin da sojojinta suka kai Damana da ke Filinge a yankin Tillaberi.

Ta kuma ta samu nasarar kwace makamai da kayan yaki da dama daga wajen 'yan bindigar.

Wakiliyar BBC da ke Yamai ta ce maharan sun zabi ranar da kasuwar Damuna ke ci domin su kai hari da zimmar haifar da mumMunar barna.

Ta ce shaidu sun ce maharan sun shigo cikin garin da babara da rana inda suka kai hari a wurare da dama da suka hada cibiyar kiwon lafiya da mai'aikatar magajin gari.

Sai dai nan take jam'ian tsaron da ke wurin su ka mayarsu mu su da martani abinda ya tilasta mu su ja da baya.