Me ya sa banki ke cajin ku idan kuka tura ko cire kuɗi?

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda bankuna ke ci gaba da yanke musu kuɗi a duk lokacin da suka ciri kuɗi ko suka tura kuɗin zuwa wasu bankuna.
Haka su ma wasu masu sana'ar cirar kuɗi na POS na ci gaba da kokawa kan abin da suka ce bankuna ta cirar musu kudi a duk lokacin da ska cire wa mutane kuɗi.
A baya-bayan nan wasu bankunan ƙasar sun ɓullo da cire wa mutane naira 25 ko naira 10 a duk lokacin da suke cire, ƙari a kan kuɗaen da aka saba yanke wa mutane.
Kan haka ne BBC ta tuntuɓi masana domin jin irin jerin kuɗaɗen da bankunan ke cirar wa mutane da kuma dalilin cirarsu su.
Ladan cirar kuɗi a ATM
Hassan Usman, tsohon Manajan na Bankin Jaiz ya ce daga cikin kuɗin da bankunan ke yankar wa mutane akwai ladan cirar kuɗi a na'urar ATM
''Idan mutum ya ciri kuɗi a na'urar ATM to akwai kuɗin da ake yankar masa, idan bankinka ne za ka yi sau uku ba tare da an yankar maka ba a cikin wata guda, amma idan ba na bankinka ba ne to za a cirar maka'', a cewarsa.
Ya ce a baya idan mutum ya ciri kuɗi a na'urar ATM ɗin da na bankinsa ba, ana yankar masa naira 60, amma yanzu CBN ya gyara dokokin inda yake yankar naira 100 daga naira 20,000 zuwa sama.
Tsohon manajan na Jaiz ya ce ana cirar wannan kuɗi ne saboda aikin da aka yi wa kwastomomi.
''Maimakon ka shiga banki ka bi layi, ka sha wahala, sai na'urar ATM ta biya maka buƙata, don haka aka ɗaukar mata ladanta'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa su waɗannan na'urori na ATM suna da matuƙar tsada sannan ga ƙarin wahalhalun da aka yi wajen kafa shi.

Asalin hoton, Getty Images
Haka ma ya ƙara da cewa akwai na'urorin banki da ake sanya wa a wasu wuraren da ba banki ba, kamar makarantu da gidajen mai, ana cirar naira 500 a kan kowane 20,000.
''Ana kuma yin hakan ne saboda kula da ɗawainiyar na'urar kasancewar ba a jikin banki take ba''.
''Su kansu na'urorin kowace guda ta kai kimanin naira miliyan 20, sannan a zo a saka mata inverter da ke ba ta wutar lantarki a kuma saka mata intanet din da za ta yi aiki, ka ga duka wanann kuɗi aka kashe don haka dole a samar da kuɗin da za a iya cike wancan giɓi'', kamar yadda ya bayyana.
Kuɗin kula da katinku na ATM
Muhammad Bello Hussaini, manajan hulda da jama'a na bankin Altenative Bank da ke Kano ya ce wannan su ne kuɗin da ake yanka domin kula da katin cirar kuɗi na ATM.
Jami'in bankin ya ce wasu bankunan kan yanki kuɗin kula da katin a kowane wata, yayin da wasu kuma suke bari sai bayan wata uku ko wani abu mai kama da haka.
Ya ce kuɗin da ake cirewa kan wannan yana kai wa naira 50.
Kuɗin bayar da katin ATM
Manajan Hulda da jama'ar na Bankin Altenative Bank da ke Kano ya ce wannan su ne kuɗin da banki ke ɗiba domin bai wa mutum katin ATM ko idan an sake masa bayan ƙarewa ko ɓacewar nasa.
''Shi wannan kuɗin sau ɗaya ake yankar wa mutum a kowane kati, wanda ake cirarsa bayan bai wa mutum katin, tun daga lokacin kuma ba za a sake cirarsu ba, har sai ya je sake katin'', kamar yadda ya bayyana.
Ya kuma ce kuɗin katin yana kamawa tsakanin naira 1,000 zuwa 1,100.
Turawa ko cire kuɗi ta zamani

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon manajan Bankin Jaiz, ya ce wannan kuɗi ne da bankuna ke yanka na ɗawainiyar da suka yi wa kwastoma na amfani da manhajojinta na yanar gizo.
Shi wannan akan yanki naira 10 ga duk kuɗin da suke ƙasa da naira 5,000 sannan naira 25 ga kuɗin da ya haura 5,000 zuwa naira 50,000, sai kuma naira 50, ga kuɗin da suka zarta naira 50,000, kamar yadda tsohon jami'in bankin ya ce.
Harajin kan-sarki (Stamp duty)
Hassan Usman ya ce wani kuɗin da bankuna ke yanka shi ne kuɗin Stamp Duty, wanda shi kuma na gwamnati ne kamar yadda ya yi bayani.
''Shi wannan naira 50 ne ga duk tura kuɗin da aka yi ta kai naira 10,000 zuwa sama'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ce shi wannan kuɗi idan banki ya ɗauka to zai tura wa gwamnatin tarayya ne.
Kuɗin tura kuɗi
Shi kuma wannan ladan hidima ne bankin ya yi maka wajen tura kuɗi zuwa wani banki, a cewar Hassan Usman.
''Kamar sauƙaƙa maka aka yi, maimakon ka je bankin ka bi layi, ka cire kuɗi, sannan ka tafi wani bankin nan ma ka bi layi domin tura wa wani, shi ne duka a aka saukaka maka wannan aka yi maka cikin sauki, shi ya sa ake cire wannan'', a cewarsa.
Kuɗin da ake yanka na wannan ya kai naira 50, zuwa sama a kan kowace naira 10,000.
Kuɗin tura saƙon banki

Asalin hoton, Getty Images
Shi ma wannan banki ne suke ɗauka domin su tabbatar wa kwastomomin cewa kuɗin da suka aika ya je, ko kuɗin da aka aiko masa sun iso bankinsa, in ji tsohon jami'in nan Jaiz.
''Kuma ko da wani ya ɗauki katinka na ATM, idan ya san lambobin sirrin da ya fara cirar kuɗin za ka ji alama, ta hanyar ji ko ganin saƙon, domin ka ɗauki matakin gaggawa, kada ya yi maka ɓarna sosai'', in ji Hassan Usman.
Ya ce bankunan kan sayi alert ɗin ne daga kamfanonin sadarwar na lambar wayar kwastomominsu.
Kuɗin cinikayyar ATM (CTO)
Tsohon manajan bankin ya ce wannan su ne kuɗin da ake cajar masu sana'ar POS, idan sun je banki ɗauko kuɗi.
Hassan Usman ya ce a yanzu an sauya wa wannan caji wa Ledger Charger, wanda ake ɗaukar wani kaso na kudin da suke ɗauka daga bankin.
Harajin VAT

Asalin hoton, AFP
Tsohon jami'in bankin ya ce su wannan wasu kuɗi ne da gwamnati ta sanya dokar cewa, a duk lokacin da aka sayi kaya kuma za a biya, to a sanya mata kashi 7.5 cikin 100 na kuɗin da aka sayi kayan.
Ya ƙara da cewa shi wannan asusun gwamnati yake tafiya bayan an gama tattara shi.
Cajin kuɗin wuta da na Talbijin
A duk lokacin da mutum ya biya kuɗin wuta ko na talbijin, ta manhajar banki, akwai naira 100 da ake ƙara wa mutum kan adadin kuɗin da ya biya.
Hassan Usman ya ce ita wannan naira 100, ta hidimar da banki ya yi maka ne, maimakon ka je ofishin wutar ka bi layi ka saya, ko kuma ka je ofishin kamfanin talbijin ɗinka, ka biya kuɗi, sai aka sauƙaƙa maka, shi ne aka ɗauki wannan naira 100 daga asusunka.











