Wane abinci aka fi son yin ciyarwa da shi a Ramadan?

- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Akwai tarin ayyukan lada da ake son musulmi ya duƙufa da yi a lokacin watan azumi na Ramadan.
Daga cikin waɗannan ayyuka akwai ciyarwa wadda yin ta ke tattare da gwaggwaɓan lada a don haka ake kwaɗaitar da musulmi su yi, in ji malamai.
BBC ta tuntuɓi fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kaduna, Sheikh Dr. Tukur Al-manar don jin bayani game da muhimmancin ciyarwa a Ramadan da kuma irin abincin da aka fi son a ciyar da su.
Abin da aka fi so a yi ciyarwa da shi
Sheikh Dr Tukur Al-manar wanda shi ne babban limamin Masallacin Jumaa na Al-Manar Kaduna ya ce babu wani zaɓaɓɓen abinci da aka fi so a ciyar da shi a watan Ramadan.
Sai dai ya ce ana son a bayar da abincin da mutanen yankin suke ci kuma suka ɗauke shi a matsayin ci-maka misali shinkafa gero masara wake da fulawa.
Ya bayyana cewa abin da ake so shi ne abincin ya zama mai kyau, nagartacce mai kuma gina jiki domin a cewarsa, "duk abin da za a bai wa Allah, ana so a bai wa Allah mafi kyawu kuma mafi inganci."
"Nau'in abinci ya banbanta daga ƙasa zuwa wata ƙasa, amma abin da a al'adance an san shi ne jama'a suke nema ruwa a jallo suke rayuwa a kai, kuma ake ce masa abinci, shi ake so a ciyar." in ji malamin.
Yadda ya kamata a yi ciyarwa

Asalin hoton, Getty Images
A cewar Sheikh Al-manar, babu wata hanya da aka zaɓa ta yin ciyarwa a Ramadan.
Ya ce "akwai waɗanda iyalai ne magidanta ne, mata ne da yaransu a gida, ya kamata a kai musu abincin a gida, a ba su, waɗanda kuma suke taruwa a masallaci, masu zuwa sai a kawo masallaci a daho shi a kawo jama'a su ci, wanda kuma za a kai gidaje a kai shi a ɗanyen sa."
A bayanin da ya yi, ga waɗanda iyalai ne, zai fi dacewa a kai musu ɗanye domin su sarrafa shi yadda suke so.
Ya kuma ƙara da cewa ga matasa da wadanda ba su da iyali, ya fi kyautuwa a ba su dafaffen abinci domin hakan zai rage musu ɗawainiya, "ba wanda za ka bai wa shinkafa ko masara, sai ya tsaya ya nemi kayan haɗi - man girki da makamantansu." kamar yadda malamin ya ce.
Muhimmancin ciyarwa a Ramadan
Sheikh Dr Tukur Al-manar ya ce akwai bambanci tsakanin ciyarwa a wasu lokutan da kuma wadda aka yi a watan Ramadan.
A wani hadisin Manzo S.A.W ya ce ''Wanda ya ciyar da mai azumi yana da ladan azumin, ba tare da an tauye wa mai azumin wani abu daga cikin ladan azuminsa ba''.
A cewar malamin, ciyarwa a watan azumi ya fi lada sosai kasancewar ana ninka ladan fiye da ciyarwar da aka yi ba a lokacin Ramadan ba.
Malaman musulunci suna jaddada irin ladan da ke tattare da ciyar da mai azumi kasancewar hadisi ya ce idan ka ciyar da mai azumi kana da kwatankwacin ladan mai azumin.
Ya ce ana son a ciyar da waɗanda samunsu bai taka kara ya karya ba ganin yadda a yanzu samu ya yi ƙaranci.











