Bellingham ya sanar da dalilin da yake sa riga mai lamba biyar

Jede Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Real Madrid, Jude Bellingham ya fadi dalilin da yake sa riga mai lamba biyar a Real Madrid.

Ya bayyana hakan a hirar da Uefa ta yi da shi a shirin da Real Madrid ke yi na karawa da Bayern Munich ranar Laraba a Champions League zagayen daf da karshe.

Bayern Munich mai kofin zakarun Turai shida za ta je Santiago Bernabeu, domin yin wasa na biyu a gasar Champions League, bayan da suka tashi 2-2 ranar Talata.

''A koda yau she mahaifina yana sa rigar Real Madrid mai dauke da lamba biyar wato wacce Zinedine Zidane ke sakawa.

Labarin abin dariya ne, domin ya sauya zuwa kaina, bayan da ya yi min kyautar rigar a lokacin da na saka hannu a kungiyar'', in ji dan kwallon tawagar Ingila.

''Na kan tambe shi, wane dan kwallo ne ke saka rigar, shi kuma ya kan ce min idan na girma zan ga sunansa a manhajjar You Tube.

Yanzu gashi ina sa riga mai lamba biyar, labari ne mai girma sosai da ba zan manta da shi ba.''

Jude Bellingham ya koma Real Madrid kan fara kakar bana daga Borussia Dortmund, kuma shi ne kan gaba a cin kwallaye a kungiyar a kakar nan.

Dan wasan tawagar Ingila ya zura kwallo 18 a La Liga, inda Real Madrid ta lashe kofin bana na 36 jimilla, saura wasa hudu a kammala kakar bana.

Real Madrid ta dauki La Liga na bana da maki 87, yayin da Girona ce ta biyu da maki 74, sai Barcelona mai rike da kofin bara da maki 73 a mataki na ukun teburi.

Dan kwallon ya saka riga mai lamba 22 a Dortmund, wanda ya fara saka lambar a Birmingham City a 2019/20.

Haka kuma dan kwallon na saka riga mai lamba 10 a tawagar Ingila, wanda ya saka lamba takwas da 22 da sauransu a baya.