Barcelona ta kasa cin Betis a La Liga a gida?

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta tashi 1-1 da Real Betis a wasan mako na 30 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar a Estadi Olímpic Lluís Companys.
Barcelona ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Gavi a minti na bakwai da fara wasan, sai dai minti na 10 tsakani Betis ta farke ta hannun Natan.
Wannan shi ne wasa na uku da suka fafata a tsakaninsu a bana, bayan 2-2 da suka tashi a La Liga ranar 7 ga watan Disambar 2024 a gidan Betis.
A wasa na biyu da suka yi a kakar nan, shi ne a Copa del Rey, inda Barcelona ce ta dura 5-1 ranar 15 ga watan Janairun 2025.
A karawa biyu baya da Betis ta ziyarci Barcelona a La Liga ta yi rashin nasara da 4-0 da kuma 5-0, amma ta ci 1-0 a kakar 2021/21 a gidan Barcelona.
Shi ne wasan da Betis ta yi nasara a gidan Barcelona a La Liga daga karawa 14 da ta kai ziyara a baya - bayan nan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta farko a kan teburin La Liga da maki 67 da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.
Ranar Asabar Real ta yi rashin nasara 2-1 a gida a hannun Valencia a wasan mako na 30 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta kakar nan.
Barcelona ta kasa cin wasa na 11 a jere a La Liga, amma ta yi karawa 22 a jere a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba tun ranar da aka shiga shekarar 2025.
Ita kuwa Betis ta yi fatan cin wasa na bakwai a jere a La Liga a karon farko a tarihi, sai dai hakan bai samu ba, wadda ta tashi 1-1 a gidan Barcelona.

Asalin hoton, Getty Images











