Liverpool na shirin miƙa tayi kan Isak, Arsenal da Chelsea na zawarcin Sesko

Asalin hoton, Getty Images
Ya na yiwuwa sai Liverpool ta biya zunzurutun kuɗi da ya kai fam miliyan 120 ko fiye ma da haka kafin ta iya ɗaukar ɗan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, daga Newcastle United - kuma za ta fuskanci hamayya daga Chelsea da Arsenal. (Give Me Sport)
Ana alakanta Arsenal da Chelsea da zawarcin ɗan wasan gaban RB Leipzig ɗan ƙasar Slovenia Benjamin Sesko, mai shekaru 21, inda ake ganin da wuya ɗan wasan ya ci gaba da zama a ƙungiyar ta Bundesliga idan har ta kasa samun gurbi a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Mirror)
Tottenham da Liverpool da Manchester City da Chelsea sun shiga jerin manyan kungiyoyin Turai da ke neman ɗan wasan Monaco ɗan ƙasar Senegal Lamine Camara mai shekara 21. (TBR Football)
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce ƙungiyar ta Bundesliga na nazarin sshiga takaran ɗaukar ɗan wasan gaban Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21, wanda ake alaƙantawa da yiwuwar komawa Manchester City a bazara. (AZ via Mail)
Real Betis na nazarin ɗaukar ɗan wasan gaba na Brazil Antony kan kwantiragin dindindin amma tana iya fuskantar ƙalubale wurin biyan albashin ɗan wasan na Manchester United, wanda aka kuma sanya wa farashin fam miliyan 41. (Fichajes)
Barcelona na sa ido kan ɗan wasan Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 20, da nufin kammala cinikin ɗan wasan na Argentina a bazara. (Fichajes)
Chelsea na shirin kammala ƙulla yarjejeniyar fam miliyan 12.4 kan ɗan wasan Brazil da Corinthians Denner Evangelista, mai shekara 17, wanda zai koma kulob ɗin da ke yammacin London a shekarar 2026. (Fabrizio Romano)
Aston Villa na fatan kammala cinikin "cikakken ɗan wasan gaba" Charalampos Kostoulas, mai shekara 17, da abokin wasansa na Girka da Olympiakos Christos Mouzakitis, mai shekara 18. (TBR Football)
Liverpool na ci gaba da bibiyar ɗan wasan Brighton Carlos Baleba don ganin yuwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiyan na ƙasar Kamaru mai shekara 21 a bazara. (Football Insider)
Chelsea da Liverpool na shirin fafatawa kan ɗaukar ɗan wasan RB Leipzig ɗan ƙasar Faransa Castello Lukeba, duk da cewa Real Madrid na cikin jerin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan mai shekara 22. (Mirror)











