An gano sabon maganin da ke kawar da ciwon haƙori cikin sauƙi

Ana wa wata mata maganin ciwon hakori

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Masu binciken da suka ƙirƙiri maganin sun ce suna fatan a samu samfurin da zai fita kasuwa a shekara mai zuwa.
    • Marubuci, Liam Barnes
    • Aiko rahoto daga, BBC East Midlands
  • Lokacin karatu: Minti 2

Sabbin bincike-bincike sun nuna cewa akwai wani sabon magani wanda yake kamar man shafawa mai ruwa-ruwa da masana suka ƙirƙira wanda zai iya taimakawa wajen gyarawa da kuma warkar da ramin haƙori, ya mayar da shi yadda yake.

Masu bincike suka ce hakan zai iya kawo sabbin hanyoyi wajen magance lalacewa ko ciwon haƙori a nan gaba.

Masana daga Jami'ar Nottingham sun haɗu da wasu masana daga sassa daban-daban na duniya domin ƙarfafa kare haƙori daga zaizayewa da yin rami da kuma hana ya ruɓewa.

Jami'ar ta ce wannan maganin da aka yi da sinadarin protein yana aiki ne ta hanyar kwaikwayon yadda ake gina ramin haƙori tun lokacin da jarirai suke tasowa. Shi ne yake zama kamar "tushen gini" ko abin da sinadarin calcium da phosphate da ke cikin yawu suke manne da shi, domin su ƙarfafa haƙori.

Ana iya karanta cikakken binciken a cikin mujallar kimiyya ta Nature Communication.

Hotunan microscope na haƙorin da ya lalace da wanda aka fara wa magani.

Asalin hoton, University of Nottingham

Bayanan hoto, Hotunan na'urar ganin ƙwayar zarra na haƙorin da ya lalace da wanda aka fara wa magani.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, fiye da mutum biliyan 3.7 suna fama da cututtukan da suka shafi baki wadanda suka samo asali daga lalacewar haƙori.

Matsalolin da kan taso sakamakon lalacewar haƙori sun haɗa da shigar cututtuka, da raɗaɗin haƙori da ma rasa haƙorin baki ɗaya, waɗanda ake alaƙantawa da wasu cutukan masu muni kamar ciwon suga da na zuciya.

Duk da cewa magungunan da ake da su yanzu kan taimaka wajen sassauta raɗaɗin ciwo amma ba sa taimakawa wajen sake cikowar kogon haƙori.

Farfesa Alvaro Mata, wanda ya jagoranci wannan bincike, ya ce sabon maganin da suka ƙirƙira "ana iya shafawa cikin sauƙi kuma cikin hanzari".

Ya ce: "Muna matuƙar farin ciki saboda an ƙirƙiri wannan maganin ne don ya zama abu mai sauƙi ga likitoci da marasa lafiya. Muna fatan fitar da samfurin farko nan da shekara mai zuwa ta yadda maganin zai iya fara amfanar mutane a fadin duniya."

Shi ma Farfesa Paul Hatton daga Sheffield ya ce tsawon shekaru kenan da masana ke ƙoƙarin samar da garkuwa ga haƙori kuma wannan bincike ya nuna cewa an samu babban ci gaba a wannan fanni.