Balde ba zai buga wa Barca wasan da za ta kara da Dortmund ba

Alejandro Balde

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta sanar cewar Alejandro Balde, ba zai buga mata wasan da za ta kara da Borussia Dortmund ranar Talata ba, sakamakon raunin da ya ji.

Ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama za ta buga wasa na biyu a Champions League zagayen kwata fainal da Dortmund a Jamus.

Ranar Laraba ne Barcelona ta caskara Dortmund da ci 4-0 a Sifaniya a gasar zakarun Turai.

Barcelona za ta buga wasan karshe a Copa del Rey ranar 26 ga watan Afirilu, inda za ta kece da Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico.

Wasu rahotannin na cewar Balde na bukatar jinyar mako uku, kafin ya koma taka leda.

Mai tsaron bayan ya ji rauni ne ranar Asabar a wasan da Barcelona ta yi nasara kan Leganes da cin 1-0.

Balde ya buga wa Barcelona wasa 43 a dukkan karawa a kakar nan da cin ƙwallo ɗaya da bayar da 10 aka zura a raga.

Barcelona tana mataki na ɗaya a kan teburin La Liga da maki 70 da tazarar bakwai tsakani da Real Madrid, wadda za ta kara da Alaves ranar Lahadi.