Me ya kamata ku yi idan gobara ta rutsa da ku?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Gobara na ɗaya daga cikin manyan haɗurran da ke iya afkuwa a gidaje, kasuwanni, ofisoshi ko hanyoyi kamar irin gobarar da ta tashi a daren ranar Talata a dogon ginin Afritower da ke birnin Legas da ta shafi ofishin hukumar tattara haraji ta FIRS da bankin UBA da kuma Capital UNited waɗanda dukkanninsu suke aiki a rukunin ginin.

Gobarar ta kashe mutum 12 tare da jikkata mutane da dama wanda ofishin FIRS ya tabbatar.

Rashin sanin yadda za a yi ko kuma rashin shiri kan yadda za a tunkari wannan hali na iya jefa rayuka cikin haɗari.

Masana sun sha yin gargadi cewa mutane su rika ɗaukar matakan kariya tun kafin ta faru, kuma su san yadda za su bi idan gobara ta tashi.

Domin sanin matakan kariya ko abubuwan da ya kamata mutane su yi i9nda sun tsinci kansu a irin wannan yanayi, BBC ta tuntuɓi Liman Ibrahim Alhaji, tsohon babban kwamandan hukumar kashe gobara na ƙasa kuma ya bayyana muhimman matakai da mutane ya kamata su sani da kuma su yi idan gobara ta tashi.

Idan gobara ta rutsa da mutane, ya za su yi?

Liman Ibrahim ya ce idan gobara ta rutsa da mutane, su yi abubuwa kamar haka;

  • Kada su firgita su fice cikin hayyacinsu.
  • Mutane su yi ƙoƙarin fita daga wurin ta hanyar kofar fitar gaggawa
  • Ficewa daga wuri cikin hanzari amma cikin tsari ba tare da gudu da turmutsitsi ba.
  • A kira hukumar kashe gobara ko lambar taimakon gaggawa.
  • A tabbatar da cewa an sanar da kowa ta hanyar buga ƙararrawar alamun gobara.
  • Kada ku tsaya don ɗaukar kaya ko waya muddin hakan zai iya jinkirta ku.
  • A yi amfani da abin kase gobara
  • Rufe ƙofofi da tagogi domin hana gobara yaduwa.

Matakan kariya kafin gobara

Tsohon babban kwamadan ya bayar da wasu muhimman matakai da za a ɗauka don rage haɗarin gobara da suka haɗa da;

  • Horar da ma'aikata a duk wata kamfani ko wurin aiki da sauran jama'a kan yadda za su fice idan gobara ta tashi.
  • Tabbatar da kayan lantarki da wayoyi suna cikin yanayi mai kyau.
  • Ariƙa yin gwaji yadda mutane za su riƙa yi idan gobara ta tashi.
  • Mutane su koyi yadda ake amfanin da abin kashe gobara.
  • A tabbatar kowanne wuri yana da ƙofar fita ta gaggawa
  • Ka guji amfani da kyandir da wutar lantarki a wuraren da ba su dace ba.
  • Ajiye abubuwan kashe gobara a gida ko ofis.
  • Sanin hanyoyin fita daga kowane wuri da kuke yawan zama.
  • Sanin yadda yadda za su kira masu agajin gaggawa.

Idan ba a samu agaji ba, ya za a yi?

Liman ya ƙara da cewa idan babu agaji a kusa, mutane su yi

  • A ci gaba da bin hanyar fita mafi sauƙi da natsuwa.
  • Kada a yi ƙoƙarin tsalle daga babbar bene, hakan na iya jawo mutuwa.
  • Idan hayaƙi ya yi yawa, ku yi ƙoƙarin ɗaukar tufafi ko zane ku rufe hanci da baki

Idan mutane sun yi yawa wajen ficewa

A wasu lokuta, mutane da yawa na iya taruwa a hanya ɗaya yayin gobara, wanda ke haifar da cunkoso da hatsari. Liman Ibrahim ya shawarci:

  • Ƙoƙarin bin tsarin layi
  • Kada a riƙa tura juna
  • Ku bar wanda ke gaba ya wuce kafin ku bi amma ku taimaka wa yara da tsofaffi su fice lafiya.
  • Haƙuri da haɗin kai na iya ceton rayuka fiye da yin hanzari.

Ya ƙara da cewa ba zai taɓa yiwuwa ba a ce wuri babu hanyoyin fita ta gaggawa ba amma ko da hakan ya kasance, "Mutane su tsaya a wuri mai aminci daga wutar sannan kada su yi ƙoƙarin tsallaka wuta kai tsaye, domin hakan na iya jefa su cikin haɗari."