Champions League: Barca ta je ta ci Benfica

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Benfica ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Barcelona a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League da suka kara ranar Laraba.

Tun a minti na 22 aka bai wa ɗan wasan Barcelona jan kati, Pau Cubarsi, kuma haka suka je hutu ba wadda ta zura ƙwallo a raga.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta ci ƙwallo ta hannun Raphinha, yayin da Benfica ta kasa farkewa.

Wannan shi ne karo na 11 da ƙungiyoyin biyu suka kece raini a gasar zakarun Turai, inda Barcelona ta yi nasara biyar da canjaras huɗu, Benfica ta ci wasa biyu.

Barcelona za ta karɓi bakuncin Benfica a wasa na biyu zagayen ƴan 16 a Sifaniya ranar Talata 11 ga watan Maris.

Barcelona tana da Champions League biyar, ita kuwa Benfica biyu ne da ita a tarihi.

Haka kuma Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga na kakar nan da maki 57, bayan cin wasa 18 da canjaras uku aka doke ta biyar.

Ita kuwa Benfica tana ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Portugal da maki 53 da tazarar uku tsakanin ta da Sporting mai jan raga.

Wasanni tsakanin Benfica da Barcelona

2024/2025

Champions League ranar Talata 5 ga watan Maris 2025

  • Benfica 0 - 1 Barcelona

Champions League ranar Talata 21 ga watan Janairun 2025

  • Benfica 4 - 5 Barcelona

2021/2022

Champions League ranar Talata 23 ga watan Nuwambar 2021

  • Barcelona 0 - 0 Benfica

Champions League ranar Laraba 29 ga watan Satumbar 2021

  • Benfica 3 - 0 Barcelona

2012/2013

Champions League ranar Laraba 5 ga watan Disambar 2012

  • Barcelona 0 - 0 Benfica

Champions League ranar Talata 2 ga watan Oktoban 2012

  • Benfica 0 - 2 Barcelona

2005/2006

Champions League ranar Laraba 5 ga watan Afirilun 2006

  • Barcelona 2 - 0 Benfica

Champions League ranar Talata 28 ga watan Maris 2006

  • Benfica 0 - 0 Barcelona

1991/1992

European Cup ranar Laraba 15 ga watan Afirilun 1992

  • Barcelona 2 - 1 Benfica

European Cup ranar Laraba 11 ga watan Disambar 1991

  • Benfica 0 - 0 Barcelona

1960/1961

European Cup ranar Talata 30 ga watan Mayun 1961

  • Benfica 3 - 2 Barcelona

Ƴan Barca 24 da suka je Benfica

Ƴan wasan Barcelona: Cubarsí, ⁠Balde, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, ⁠Pedri, ⁠Lewandowski, ⁠Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña da kuma ⁠Pablo Torre.

Sauran sun haɗa da Fermín, M. Casadó, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, ⁠F. De Jong, Kounde, Eric, ⁠Szczęsny, Kochen, H. Fort da kuma Gerard Martín.