...Daga Bakin Mai Ita tare da Giɗaɗo na shirin Daɗin Kowa
Daga Bakin Mai Ita, wani shiri ne na BBC Hausa, da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
An haifi Abdul M. Nazari a cikin ƙaramar hukumar Shira ta jihar Bauchi, kuma ya ce a can ya fara karatunsa na Firamare da Sakandire.
Abdul wanda aka fi sani da sunan Giɗaɗo a fitaccen shirin Daɗin Kowa na gidan talbijin ɗin Arewa24, ya ce haƙiƙa karatunsa na boko bai yi nisa ba, kuma a ƙoƙarinsa na neman abin yi ba tare da ya dogara ga aikin gwamnati ba, shi ne ya shiga harkar fim.
Ya ƙara da cewa bai yi fina-finai da yawa ba, amma yana da burin ya yi aiki tare da fitaccen jarumin nan Adam A. Zango.
Abdul M. Nazari ya ce ko da yake ba ya jin Fulatanci, amma ƙudurinsa na cewa duk abin da mutum ya sa kansa, to yana iya yi, har ma ya yi fice, hakan ta ba shi ƙwarin gwiwar taka rawar Bafulatani a shirin Daɗin Kowa.
Baya ga sana'ar fim, Abdul ya ce yana kuma yin ɗinki. Ya ƙara da cewa babban burinsa shi ne ya zama mashahurin mawaƙi a masana'antar Kannywood.
Ku dai saurari zantawar a wannan bidiyo na sama don jin....daga bakin mai ita.








