Ƙafafuna ba su iya riƙe ni idan na tuna halin da yarana ke ciki - Chefsafmar

Aisha Kabir da mijinta

Asalin hoton, Instagram/Chefsafmar

Bayanan hoto, Aisha Kabir da mijinta kenan suke neman taimako da yin bayanin abin da ya faru cikin wani bidiyo da suka wallafa a shafukan zumunta
Lokacin karatu: Minti 3

Aisha Kabir da aka fi sani da Chefsafmar ta faɗa halin da babu wata uwa da za ta so ta tsinci kanta a ciki sakamakon sace mata 'ya'ya huɗu da masu garkuwa suka yi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Yanzu haka 'ya'yan nata na hannun masu garkuwar yayin da take jinyar tagwayen da ta haifa 'yan wata biyu.

A daren Talatar da ta gabata ne mutanen waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kutsa gidanta tare da ɗauke yaran huɗu - uku mata, ɗaya namiji ɗan ƙasa da shekara biyu.

Wannan lamari na ɗaya daga cikin sace-sacen al’umma na baya-bayan nan da ya tayar da hankulan al’umma a faɗin arewacin Najeriya, yankin da ke fama da matsalar ƙungiyoyin ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Tuni masu garkuwa da yaran suka buƙaci a biya naira miliyan 300 a matsayin kuɗin fansa ko kuma su illata su, kamar yadda Aisha ta shaida wa BBC.

Takalma a kwata

Aisha Kabir shahararriyar mai girke-girke ce a shafukan sada zumunta, inda take amfani da sunan Chefsafmar a Instagram, kuma mazaunan unguwar Keke ne da ke cikin birnin Kaduna a arewacin Najeriya.

Ta faɗa wa BBC cewa an sace yaran ne daidai lokacin da take jinyar jariran da ta haifa tagwaye a asibiti.

"Iina asibiti lokacin da mahaifinsu ya koma daga gidan gona kuma ya tarar ba su nan," kamar yadda ta fara bayyanawa cikin rawar murya da kuka.

"Da misalin ƙarfe 9:00 na dare ya kira ni yake tambayata ko sun faɗa min za su je wani wuri. Na kira 'yar'uwata, da mahaifiyarmu duka suka ce min ba su je gidansu ba.

"Sai aka fara bin maƙobta ana tambaya. Su ma duka suka ce ba su gidan, daga baya kuma sai aka ga takalmansu a cikin kwata (kwatami)."

A cewarta, daga baya mahaifin yaran ya lura da yadda aka karya ƙofar gidan ta baya.

'Abin da yaran suke faɗa mana ta waya'

Yaran da yanbindiga suka yi garkuwa da su a Kaduna.

Asalin hoton, Aisha Kabir/Chefsafmar

Bayanan hoto, Yaran da masu garkuwa suka sace a Kaduna.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babba daga cikin yaran mace ce mai shekara 14, mai bi mata tana shekara 12, ta ukun shekararta bakwai, sai kuma namiji kuma ƙaramin cikinsu mai shekara kusan biyu.

Baya ga yaran da miyagun suka sace, sun kuma haɗa da wayar da iyayensu ke bar wa yara a gida, wadda da ita ne suke kiran Aisha da mijinta domin su faɗa musu abin da suke buƙata.

Ta ce ba ta iya jure jin muryarsu a waya, dalilin haka sai dai mahaifinsu ne kawai yake magana da su.

"Lokacin da suka kira na farko wallahi ƙafafuwana sun kasa riƙe ni saboda firgici da na ji muryarsu; ina tunanin to su da suke kallon yaron ido da ido ya suke ji," in ji Aisha.

"Akwai lokacin da mahaifinsu ya yi waya da su a gabana, sun bai wa babbar wayar cikin kuka tana cewa: 'dady sun ce idan ba a kawo kuɗi ba za su kashe mu, kuma muna jin yunwa, babu ruwa'."

Ta ce yanzu haka suna cikin halin damuwa.

"Akwai damuwa sosai; a ce mu da muke cikin gida muna jin sanyi na shigowa, mu ɗauki bargo ka lulluɓa, to su da suke can da bindigogi a kansu wane irin hali yarana ke ciki?"

Shakka babu wannan lamari zai tuna wa 'yan Najeriya labarin Hanifa 'yar shekara biyar da aka gano gawarta a watan Janairun 2022, bayan wani malamin makarantarsu ya sace tare da kashe ta, kuma ya binne gawarta.