Yadda majalisun dokokin Najeriya suka zamo 'yan amshin shata - CISLAC

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE
A Najeriya, ana ci gaba da muhawara bayan bayyanar wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna ɗan majalisar dattawan ƙasar sanata Adams Oshiomole, na zargin majalisar dattawa da zama 'yar amshin Shata, bisa ga yadda take amincewa da duk wani ƙudurin doka da aka gabatar mata cikin gaggawa.
Oshiomole ya ce akwai buƙatar gudanar da zazzafar muharawa kan kowacce doka kafin amincewa da ita.
Adams Oshiomole ya bayyana matuƙar damuwarsa, ya na mai cewa babbar illa ce a ce 'yan majalisa ba sa tsayawa su yi zazzafar muhara akan duk wata doka ko wani ƙudurin doka da aka gabatar musu.
Wannan lamari dai ya ja hankalin ƙungiyoyin fararen hula a ƙasar in da suka ce ba sabon abu bane kasancewar majalisun dokokin Najeriyar 'yan amshin shata.
Malam Awwal Musa Rafsanjani, shi ne shugaban ƙungiyar CISLAC, mai lura da ayyukan 'yan majalisa da shugabanci nagari a Najeriya ya shaida wa BBC cewa, a shekarun baya da suka wuce an ga yadda ake kawo ƙudurori gaban majalisa musamman ta dattawa kuma ba tare da ɓata lokaci ba sai ta zartar.
Ya ce," Wani lokaci ba a tattaunawar da ta dace har wasu 'yan majalisar su san cewa ma ga abin da aka kawo ake son a tattauna akai, kawai waɗanda ke zaman majalisar ne a ranar ke rattaba hannu akan cewa an amince da ƙudurin da aka kawo."
Shugaban na CISLAC, ya ce "ba wani abu ke janyo haka ba sai don kawai wannan ƙuduri ya zo daga wajen shugaban ƙasa ko kuma daga fadar shugaban ƙasar ne shi ya sa ba tare da ɓata lokaci ake amincewa da shi, wannan sam ba dai-dai ba ne."
Ya ce,"abin da Oshiomole ya yi magana akai abu ne da ya dace ace na tsaya na yi nazari akai, domin an san majalisa da cikakkiyar muhawara da tabbatar da cewa duk wata doka da majalisar ta yi ta na tabbatar da cewa an yi ta ne da amincewar 'yan kasa."
"A don haka 'yan ƙasa na kallon abin da ƴan majalisar ke yi, da kuma abin da ke faruwa, kuma hakan da majalisun ke yi to ko shakka babu na zubar musu da ƙima da martaba a idanun 'yan kasa." In ji shi.
Sanata Oshiomole, ya taso da wannan bayanin ne a wani zama da majalisar ta yi in da aka gabatar da ƙudurorin dokokin da suka shafi jarabawar kammala makarantar sakandire ta NECO da aka tilastawa dukkan daliban makarantun sakandiren ƙasar rubutata, sai ƙudurin da ya shafi samar da wata hukumar kula da nazarin ilmin addinin musulunci da harshen Larabci.
Bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Opeyemi Bamidele ya gabatar da ƙudurorin, sai kawai aka amince da su a rana daya, ba tare da samun zazzafar muhawara ba, hakan ya sa sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa tsarin na da tasgaro sosai.
Ƙungiyoyin fararen hular dai na ganin muddin ba a yi wa tufkar hanci ba, to ko babu shakka hakan zai kai kasar ya baro.











