'Kowace rana ji nake tamkar ita ce ta ƙarshe' - Ɗan Isra'ilan da ya kuɓuta daga Hamas

Kaid Farhan Elkadi.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Kaid Elkadi ne mutum na takwas cikin jerin mutanen da sojojin Isra'ila suka kuɓutar
Lokacin karatu: Minti 4

Makiyayin Balaraben da aka kuɓutar daga Gaza ya buƙaci Isra'ila ta cimma yarjejeniya da Hamas domin sakin duka sauran Isra'ilawan da ƙungiyar ke garkuwa da su, yayin da ya bayyana irin halin da ya shiga lokacin da yake Gaza.

An kuɓutar da Kaid Farhan Elkadi, mai shekara 52, ranar Talata, a wani hari da sojojin Isra'ila suka kira mai cike da sarƙaƙiya a kudancin Zirin Gaza.

Bayan komawarsa ƙauyensu da ke kudancin Isra'ila ranar Laraba, Elkadi ya ce ''farin cikinsa ba zai cika ba, matsawar akwai ragowar mutanen da ake garkuwa da su'' a duka ɓangarorin.

Tsohon magajin garin Isra'ila, ya ce zai yi wahala mista Elkadi ya shiga rana har nan da wata takwas.

A wani labarin na daban a ranar Laraba, Isra'ila ta ce ta gano gawar wani sojanta da aka kashe tun a harin watan Oktoban bara da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila.

To sai dai sojojin ba su fitar da cikakkun bayanan sojan ba kamar yadda iyalansa suka buƙata.

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce ''girman hare-haren'' do sojojin ƙasar ke ƙaddamarwa tare da sauran jami'an tsaron ƙasar na nuna irin ''ƙaimin da muke da shi na kuɓutar da sauran mutanen''.

Amurka da Masar da Qatar na ƙoƙarin shiga tsakani domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta bayar da damar sakin duka mutane 103 da Hamas ke garkuwa da su - ciki har da mutum 33 da ake tunanin sun mutu - ta hanyar musayar fursunoni Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mayaƙan Hamas sun yi garkuwa da mista Elkadi a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoba da suka kai cikin Isra'la, kuma shi ne mutum na takwas da sojojin Isra'ila suka kuɓutar tun bayan fara yaƙin Gaza.

A ranar Laraba ne ya isa ƙauyensu da ake kira Karkur a yankin hamadar Negev bayan an sallame shi daga asibiti.

Yayin da 'yan uwa da abokan arziki da manema labarai suka zagayen shi don yi masa barka, mista Elkadi ya yi kiran da a saki duka ragowar mutanen da ake garkuwa da su.

“Ba tare da la'akari da ƙabilarsu ba, (ko Larabawa ne ko Yahuwada), dukkansu suna da dangin da ke jiran fitowarsu. Kuma su ma suna buƙatar samun 'yanci da farin ciki.

"Ina fata, kuma ina addu'ar kawo ƙarshen wannan," in ji shi, ya ce wannan saƙon ya sanar wa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a lokacin da ya yi waya da shi ranar Talata bayan kuɓutar da shi.

"Na kuma shaida wa maiɗakin Netanyahu jiya cewa: ‘a yi ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan abu.”

An ƙyale Mista Elkadi ya koma gida ne bayan yi masa jerin gwaje-gwaje a asibiti.

Tun da farko, Elkadi mai ƴaƴa 11 ya shaida wa ƴan'uwansa ''irin uƙubar da ya sha a a kwanakin da ya kwashe ana garkuwa da shi'', kamar yadda Ata Abu Medigam , tsohon magajin garin Rahat da ke kudancin ISra'ila ya shida wa jaridar Haaretz ta Isra'ila.

"Ya yi magana kan wani mutum da aka tsare su tare na tsawon wata biyu, wanda kuma ya mutu a gabansa," in ji mista Medigam.

Ya ƙara da cewa mista Elkadi ya kuma fara fargabar rasa ganinsa a lokacin.

"Dole ne ya je a duba idanunsa don tabbatar suna gani yadda ya kamata'', in ji shi

Sojojin Isra'la sun ce sun gano Mista Elkadi a wata hanyar ƙarkashin ƙasa,'' shi kaɗai ba tare da kowa ba''.

Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun ce ba za su wallafa cikakkun bayanan yadda aka kuɓutar da shi ba, ''saboda barazanar da sauran mutanen da ake garkuwa da su, ka iya fuskata, da kuma dalilai na tsaron sojojinmu da ma tsaro ƙasar baƙi ɗaya''.

To sai an samu wasu bayanai dangane da halin da mista Elkadi ya shiga lokacin da ake tsare da shi.

Ɗan'uwansa mai suna, Fad Abu Sahiban, ya ce mista Elkadi bai samu wani sassauci daga Hamas ba, duk da kasancewarsa musulmi.

"Bai samu wani sassauci ba duk da kasancewarsa Musulmi. Ya ce sallah kawai suke barin sa ya yi, ban da ita babu wani sauƙi da yake samu daga gare su," kamar yadda ya shaida wa Haaretz.

Mista Elkadi bai samu damar yin magana da kowa ba, kuma a koyaushe yakan ji ruwan bama-bamai a kansa, in ji ɗan'uwan nasa.

''Yana jin saukar hare-haren jami'an tsaron Isra'ila, inda ya ce jikinsa kan ɗauki rawa a duk lokacin da ya ji hakan'', in ji Abu Sahiban.

"A kowace rana ji yake tamkar ita ce ranarsa ta ƙarshe a duniya, ba wai saboda masu garkuwa da shi ba; sai dai don irin hare-haren da sojojin Isra'ila ke ƙaddamarwa. Ya ce a kowace rana cikin barazanar mutuwa suka."

Mista Elkadi, wanda ya kwashe shekaru yana aiki a matsayin mai gadin ƙofar Kibbutz da ke kusa da kan iyakar Isra'ila da Gaza, wurin da aka sace shi.

Dakarun sojin ISra'ila sun ƙaddamar da hare-hare da nufin wargaza Hamas, a wani mataki na mayar da martani kan harin ranar 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar ta kai kudancin Isra'ila, lamarin da ya yi sanadin kisan kusan mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 251.

Fiye da mutum 40,30 ne ka kashe a Gaza tun bayan fara yaƙin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana.

A baya-batyan nan an ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Masar da nufin sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

To sai dai babu alamun cimma nasarar tsagaita wutar kawo yanzu sakamakon tarin sharuddan da ke tattara da buƙatar hakan.

Daga ciki akwai buƙatar Netanyahu na barin sojojin Isra'ila a kan iyakar Masar da Gaza, wani abu da Hamas ta yi watsi da shi.

Akwai kuma wasu makiyayan Larabawan biyu, Yousef Zyadna tare da ɗansa, Hamza, da har yanzu ke raye a hannun masu garkuwar, to amma na ukunsu Mhamad el-Atrash, ya mutu a hannun Hamas, kuma har yanzu tana ci gaba da riƙe gawarsa.

Haka ma akwai wani makiyayin mai suna Hisham al-Sayed, da aka kama tun 2015 kuma har yanzu yake Gaza.