Tottenham ta kammala sayen Solanke daga Bournemouth

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta sayi ɗan wasan tawagar Ingila, Dominic Solanke daga Bournemouth kan fan miliyan 65.
Ƙungiyar za ta biya fam miliyan 55 da karin fam miliyan 10 ga ɗan wasan mai shekaru 26, wanda ya rattaba hannu kan kwantiragi zuwa karshen kakar 2030.
Solanke, wanda ya buga wa Ingila wasa ɗaya, shi ne na huɗu da Tottenham ta ɗauka a bana, bayan Yang Min-hyuk da Lucas Bergvall da kuma Archie Gray.
Kocin Tottenham, Ange Postecoglou na karfafa gurbin masu cin ƙwallaye a ƙungiyar, tun bayan da Harry Kane ya koma Bayern Munich a bara.
Solanke ya koma Bournemouth kan fan miliyan 19 a shekarar 2019 daga Liverpool.
Ya taka rawa mai ban sha'awa a kakar 2023-24, inda ya zura ƙwallo 21 a wasa 42.
Ana sa ran Solanke zai halarci wasan sada zumunci da Tottenham za ta yi da Bayern Munich ranar Asabar.
Zai iya buga mata wasan farko a gasar firimiya a karawar da Tottenham za ta yi da Leicester City a King Power ranar 19 ga watan Agusta.
Solanke ya fara daga karamar ƙungiyar Chelsea - sau biyu ya lashe gasar cin kofin matasa na FA - amma wasa ɗaya ya yi a babbar ƙungiyar a kakar 2015-16 daga baya aka bayar da aronsa ga Vitesse Arnhem.
Ya koma Liverpool ne a watan Mayun 2017 bayan kwantiraginsa ya kare a Stamford Bridge, amma ya ci kwallo ɗaya kacal a wasa 21 da ya buga wa ƙungiyar Anfield.
Solanke ya taimaka wa Ingila ta lashe kofin duniya na ƴan kasa da shekaru 20 a shekarar 2017 kuma shi ne ya karɓi ƙyautar fitatcen ɗan wasa a gasar.
Ɗan wasan wanda haifaffen Reading ne ya koma Bournemouth a watan Janairun 2019, ya zura kwallo 77 a wasa 216 a kungiyar.











