Liverpool na neman Olise don maye gurbin Salah, Arsenal da United na kokawar ɗaukar Adeyemi

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gefe na Bayern Munich Michael Olise, ya nuna sha'awarsa na taka leda a Liverpool, Arsenal da Manchester United na kokawar ɗaukar ɗan wasan gaban Borussia Dortmund Karim Adeyemi, Newcastle na neman ɗan wasan tsakiya na Alkmaar Kees Smit,
Liverpool na duba yiwuwar ɗaukar dan wasan Bayern Munich Michael Olise, 23, a matsayin ɗan wasan da zai maye mata gurbin Mohamed Salah, 33. (Fichajes in Spanish)
Arsenal ta shiga cikin jerin masu neman siyen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund's Karim Adeyemi, 23, tare da Manchester United. (Teamtalk)
AZ Alkmaar za ta bar ɗan wasan tsakiyar Jamus Kees Smit, ya tafi, amma ta na son siyar da shi ga Newcastle, ko Real Madrid, ko Barcelona, ko Bayern Munich, da dukkan su suka nuna sha'awar siyen ɗan wasan, kan fam miliyan 22.(Sky Sports)
Paris St-Germain na harin siyen ɗan wasan gaban Brazil Vinicius Jr, a kakar wasa mai zuwa ta 2027, bayan kwantaragin ɗan wasan da Real Madrid ya ƙare. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan gaban Arsenal da Brazil Gabriel Jesus, 28, ya nuna sha'awarsa na komawa tsohuwar ƙaungiyar sa ta Palmeiras a nan gaba don taka leda. (Mirror)
Newcastle na kokawar ganin ta siye James Trafford, 23, a watan Janeru mai zuwa, yayin da mai tsaron ragar ke ci gaba da kokawar samun gurbin buga wasa a Manchester City. (Teamtalk)
Liverpool da Juventus na sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Bayern Munich da Jamus Serge Gnabry, 30, da kwantaraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar wasanni. (Bild - in German)
Manchester City, da Liverpool da Tottenham na sa ido kan ɗan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, 25, don ganin sun siye shi a kakar cinikin ƴan wasa, da za a fara a watan Janeru. (Sky Sports)
Liverpool na son siyen ɗan wasa bayan Bayern Munich da Fransa Dayot Upamecano, 27, da kwantaraginsa zai ƙare a kakar siyar da ƴan wasan mai zuwa. (Metro)
Ɗan wasan bayan Newcastle da Switzerland Fabian Schar, 33, na sha'awar komawa gasar Bundesliga idan kwantaraginsa ya ƙare a kakar wasa mai zuwa. (Florian Plettenberg)
Juventus na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wassan tsakiyar Lille da Fransa mai shekaru 18 Ayyoub Bouaddi, amam sai da za ta iya janyewa saboda farashin da aka sanyawa ɗan wasan na fam miliya 35. (Corriere dello Sport - in Italian)
Leicester City na neman sabon daraktan tsare-tsare, da zai kula da ɗuko ƴan wasan, don yin garam bawul a tsarin tafi da ƙungiyar. (Telegraph - subscription required)











