Chelsea ta amince da sayen Quenda kan fan miliyan 40

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nizaar Kinsella
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubucin wasanni na BBC Sport
- Lokacin karatu: Minti 1
Chelsea ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗanwasan gefe na ƙungiyar Sporting, Geovany Quenda.
Ana sa ran ɗan shekara 17 zai saka hannu kan yarjejeniyar shekara bakwai a Stamford Bridge da kuma zaɓin ƙarin shekara ɗaya kan kuɗi fam miliyan 40.
Chelsea na da 'yanwasan da za ta iya amfani da su a duka gefunanta amma ta amince cewa Quenda, wanda sai 2026 zai koma, na da basirar buga kowane gefe.
Ɗanwasan tawagar Portugal ta 'yan ƙasa da shekara 21 ya ci ƙwallo biyu tare da bayar da takwas a ci cikin wasa 43.
An sha alaƙanta shi da komawa Manchester United domin haɗewa da tsohon kocinsa Ruben Amorim.
Joao Paiva na kafar yaɗa labarai ta CNN Portugal ya ce Quenda ne "matashin ɗanwasa mafi hazaƙa" a Portugal yanzu haka.
"Mun fara jin labarin Quenda 'yan shekaru da suka wuce lokacin da yake shekara 14 ko 15 a gasar matasa ta Sporting, saboda yana da basira, da ƙwarewa, da kuma hanzari.
"Muna ganin sa a matsayin ɗanwasa mai kyau sosai, amma kuma zai buƙaci ƙarin horo sosai."











