Ƙungiyoyin Saudiyya na fatan ɗauke Salah, Roma na zawarcin Zirkzee

Salah lokacin ɗaukar horo da tawagar Liverpool a ranar Litinin. Ɗanwasan ya koma Liverpool ne daga Roma a 2017

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Gasar Saudi Pro League za ta yi "duk abin da ya dace" domin ganin ɗanwasan gaban Liverpool da Masar, Mohamed Salah mai shekara 33, ya koma taka leda a Saudiyya a cikin watan Janairu. (Gulf News)

Ɗanwasan gaban Bournemouth da Ghana mai shekara 25, Antoine Semenyo, ya zaɓi komawa taka leda a Liverpool.(Team Talk)

Semenyo ya juya baya ga Tottenham, yayin da Arsenal da Manchester City ke ci gaba da bibiyar ɗanwasan. (Sun)

Ɗanwasan bayan Crystal Palace, Marc Guehi, na fatan komawa Liverpool amma Barcelona ta shiga zawarcin ɗanwasan Ingilan mai shekara 25.(Team Talk)

Aston Villa na bibiyar ɗanwasan gaban Brazil mai shekara 19, Alysson, wanda ke taka leda a Gremio. (The Athletic - subscription required)

Roma ta shiga tattaunawa da Manchester United kan ɗanwasan gaban Netherlands mai shekara 24, Joshua Zirkzee. (Sky Sport Italia)

Manchester United na zawarcin ɗanwasan bayan Austrian da Elche mai shekara 24, David Affengruber. (Team Talk)

Ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 30, Jack Grealish, na jin daɗin zama a Everton kuma yana fatan ci gaba da aiki tare da koci David Moyes. (Football Insider)

Liverpool da Chelsea na zawarcin ɗanwasan gefen RB Leipzig da Ivory Coast, Yan Diomande, mai shekara 19, wanda ake ganin tsadar shi za ta kai (£69m-£87m). (Fichajes - in Spanish)