Yadda ake nazarin farfaɗo da finafinai a Kano

Cibiyar bunƙasa harsunan gida ta hanyar kasuwanci da shagulgulan finafinan Afirka da ke Kano a Najeriya na ci gaba da gudanar da wani babban taron shagalin finafinai na kwana shida, wanda aka fara a farkon makon nan.
Masu shirya finafinai da bayar da umarni na ciki da wajen Najeriya ne ke halartar taron, sannan kuma a gefe guda ana bajekolin zane-zanen al’adu da kuma kayan abincin gargajiya da kuma tufafi.
Bayanai na cewa jihar Kano wuri ne da ake gudanar da harkokin finafinai kuma ɓangaren shi ne matsayin na uku wajen samar da ayyukan yi a jihar.
Bikin wanda ke ci gaba da gudana, na kokarin bunƙasa ɗumbin al'adun Kano da sauran yankunan Afrika ta hanyar finafinai da mayar da hankali kan dakumantari na al'ada don inganta al'adun gargajiya na yankin da kuma bunkasa samun kudi a safar.
Jagoran shirya kalankuwar finafinan harsunan Afrika a Kano Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya shaida wa BBC cewa suna duba yanayin da ake ciki ne na komawa kan tsarin intenet shi ya sa suka yunƙuro, "Idan muka yi sake za a zo a mamaye abubuwan da muka gada daga iyaye da kakanni na ɗabi'unmu da rayuwarmu."
Alhaji Abdulkareem Muhammad ya ce suna ƙoƙarin horas da matasa wajen ganin sun riƙa amfani da harshensu a duk inda suka samu kan su, "saboda idan ana amfani da harshe to za a kiyaye bacewarshi daga doron ƙasa."
Cikin wannan babban taro dai, akwai bangaren da ake koyar da masu shirya finafinai dabarun aiki tun daga yadda ake mayar da rubutaccen labari zuwa fim kuma ya gamsar da masu kallo.
Dr Musa Abdullahi Sufi daya daga cikin masu gabatar da lakca a taron ya gabatar da maƙala kan yadda finafinan Kannywood ke bada gudumuwa wajen, 'Canza wa mutane tunani musamman kan shugabanci."
Kazalika, taron harkokin finafinan Afrikan ya tattauna matsaloli da harkokin shirya finafinai ke fama, musamman Kannywood, inda aka yi dogon nazari.
Ado Ahmad Gidan Dabino na cikin masu halartar taron ya kuma ce sun fahimci cewa takara rawa a finafinai na buƙatar mutum ya ƙara da baiwar da yake da ita wajen aiwatar da abunda ake buƙata.
Raihana Alhassan marubuciya ce kuma ta ce taron ya kara bude mata tunani ta yadda za ta ci gaba da kirkirar labarai masu kayartarwa.
A gefe guda kuma wanann babban taron wani dandamali ne na gasar nuna finafinan da aka yi su da harsunan Afrika, inda aka sanya wani ma’auni da za a zabi finafinan guda goma sha shida da za a ba su lambar yabo cikin finafainai fiye da dari biyar da suka shiga gasar daga kasashe talatin da biyar.
Kuma a ranar asabar 30 ga wannan wata na Nuwanba ne ranar da za a rufe taron, za a bayyana finafinan da suka yi nasara.











