California ta zama ta huɗu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya

Birnin California

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihar California na kan gaba a masu adawa da haraje-harejen Trump
Lokacin karatu: Minti 3

Tattalin arzikin Birnin Carlifornia ya zarta na ƙasar Japan, lamarin da ya sa jihar Amurkan ta zama ta huɗu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya

Gwamnan jihar, Gavin Newsom ya nuna cewa sabbin alƙaluma daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF da bayanai daga Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Amurka sun tabbatar da bunƙasar tattalin arzikin birnin.

Alƙaluman sun nuna cewa a shekarar 2024 arzikin da ake samu a cikin jihar (GDP) ya kai dala tiriliyan 4.10, lamarin da ya sa ya zarta na ƙasar Japan, wadda ta samu dala tiriliyan 4.01 a shekarar.

A yanzu haka jihar na bin bayan ƙasashen Jamus da China da kuma Amurka a fannin bunƙasar tattalin arziki.

"A yanzu California ta wuce a ce tana neman zama wani abu a duniya, saboda ta riga ta zama', a cewar Gwamna Newsom.

Wata yarinya na wasa da takalmin taya

Asalin hoton, Getty Images

Sabbin alƙaluman na zuwa ne yayin da Newsom ke suka kan sabbin harajin da Shugaba Trump, inda ya nuna damuwarsa kan makomar tattalin arzikin ƙasar.

Jihar California na da kaso mafi tsoka a ɓangaren masana'antu da fannin noma a Amurka.

Haka kuma jihar ta kasance kan gaba a fannin fasahar zamani, kuma cibiyar nishaɗantarwa ta duniya, sannan ta biyu mafi yawan tasoshin jiragen ruwa a Amurka.

Newsom, fitaccen ɗan jam'iyyar Democrat, wanda ake ganin zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa a 2028, ya shigar da ƙara domin ƙalubalantar ikon Trump na ƙaƙaba harajin da ya haifar wa duniya rikicin kasuwanci.

Shugaba Trump ya ƙaƙaba harajin kashi 10 kan kayyakin ƙasashen duniya da ke shiga Amurka, bayan dakatar da babban harajin da ya sanya na tsawon wata uku.

Haka kuma Shugaba Trump ya sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan kayyakin Mexico da Canada.

Yayin da harajin da ya sanya wa kayyakin China ya haifar da rikicin kasuwanci tsakanin Amurkan ta ɗaya da kuma China ta biyu a ƙarfin tattalin arziki.

Trump ya sanya harajin kashi 145 kan kayayyakin China da ke shiga Amurka, yayin da ita kuma China ta mayar da martani da kashi 125 kan kayayykin Amurka da ke shiga ƙasarta.

Birnin California

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, California na samun arzikin cikin gida da ya kai dala tiriliyan 4.10
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Newsom ya bayyana damuwarsa kan makomar tattalin arzikin jiharsa.

"Yayin da muke farin ciki dangane da wannan nasara da muke samu, a ɗaya gefen kuma nasarar tamu na fuskantar ƙalubale sakamakon haraje-haraje da gwamnatin tarayya ta ɓullo da su,'' in ji gwamnan.

"Tattalin arzikin California ya zarta na wasu ƙasashen, don haka dole a kare shi.''

Trump ya ce yaƙinsa na kasuwanci na da hujja saboda cike giɓin shekarun da aka ɗauka ana more wa Amurka a fannin kasuwanci.

Ya ƙara da cewa an sanya ƙarin harajin ne da nufin ƙarfafa wa kamfanonin ƙasar gwiwa domin ƙara samar da ayyuka a ƙasar.

Harajin na ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren tattalin arzikinsa, saboda yadda ya rage kuɗin ruwa, da nufin rage basuka ga Amurka.

Sabbin alƙaluman sun nuna cewa arzikin da California ke samu a cikin gida ya kai dala tiriliyan 4.10, kuma shi ne na huɗu a duniya, bayan na Amurka mai dala tiriliyan 29.18 da China mai dala tiriliyan 18.74 sai kuma Jamus mai dala tiriliyan 4.65.

Alƙaluman sun kuma nuna cewa tattalin arzikin California ne kan gaba wajen haɓaka tsakanin ƙasashen duniya.

Tattalin arzikin Japan na cikin tsaka mai wuya, sakamakon raguwar yawan al'ummar ƙasar, abin da ke nuna cewa guraben ayyuka na ci gaba da raguwa.

A makon nan ne Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Japan, tare da bayar da shawara ga babban bankin ƙasar na ƙara kuɗin ruwa, domin magance illar da ƙarin harajin Amurka zai yi wa ƙasar.