An rage hukuncin tara da dakatarwar da aka yi wa Mourinho

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafar Turkiya ta rage hukuncin biyan tara da dakatarwa wasa huɗu da ta yi wa Jose Mourinyo, yanzu ya koma biyu.

Hakan ya biyo bayan ɗaukaka kara da ƙungiyarsa ta Fenerbahce ta yi.

An kuma rage biyan tarar da aka yi wa ɗan kasar Portugal daga Lira 1.6m (£35,000) ya koma Lira 558,000 (£12,200).

Ƙungiyar ta Mourinho ta sanar tun ranar Alhamis cewar za ta ɗaukaka kara, bayan da aka hukunta shi karo biyu, sakamakon wasan da aka tashi 0-0 tsakanin Galatasaray da Fenerbahce ranar Litinin.

A karawar ce aka kawo alkalin wasa ɗan kasar Slovenia, Slavko Vincic ya busa wasan, bayan da ƙungiyoyin suka amince a gayyato wani daga wajen kasar.

Sai dai raflin da ya yi zaman ko-ta-kwana na Turkiya ne, Mourinho ya ce da alkalin ɗan kasar Turkiya ne da an tashi da takaddama a fafatawar.

Yanzu dai Mourinho ba zai ja ragamar wasan Lahadi ba da Antalyaspor, tun farko bai jagoranci Turkish Cup da Gaziantep ba ranar Asabar.

Ranar Juma'a Mourinho ya shigar da kara, inda ya bukaci Galatasaray ta biya shi Lira 1,907,000 kimanin £41,000 - bayan da ta zarge shi da yin kalaman wariya.

Mourinho ya faɗa cewar bayan da aka tashi wasan na hamayya, masu masauƙin baƙi na yin rawar murna kamar birrai.

Fenerbahce tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Turkiya da maki shida tsakani da Galatasaray mai jan ragama.