Yadda azumin musulmi ya bambanta da na kirista

...

Asalin hoton, Getty Images

A wannan shekarar, azumin da musulmi da kirista suke yi ya faɗo kusan lokaci ɗaya. An soma azumin kiristoci (Lent) ranar 14 ga watan Fabarairu kuma za a gama shi a ranar 28 ga watan Maris yayin da al'ummar musulmi suka soma nasu azumin na tsawon kwana 29 ko 30.

Ga waɗannan abokan juna, Seydou da Alphonse, wannan na nufin za su sauya tsarin cin abincinsu musamman abincin dare na ranar Juma'a a gidan Seydou na haɗaɗɗen dambun gero da nama da ake kira "thiere".

"Idan na yi tunanin zan yi kewar haɗuwarmu don cin dambun na tsawon fiye da wata ɗaya, sai na ji ba daɗi," in ji Alphonse, yana magana ba tare da wasa ba. Ya na azumin lent kuma ba zai ci abinci ba a ranar Juma'a.

Seydou ya ba shi tabbacin: "Amma aƙalla kana iya cin wani abu, sannan ka sha lokacin da kake so. "Ƙishirwa ce ke sa Ramadan wahala.

Hirar tsakanin waɗan nan abokan biyu da dukkansu ke azumi kamar yadda addininsu ya umarta, ta yaye labule game da bambancin azumin nasu.

Asalin azumin kiristoci...

…

Asalin hoton, Getty Images

Azumin Lent ana yin shi ne tsawon kwana 40 inda a kwanakin kiristoci ke tunawa da abubuwan da suka faru lokacin mutuwar Yesu wanda rayuwarsa da koyarwarsa suka zama tushen kiristnaci.

Kirsitoci sun yi amannar cewa hakan na nuna irin sadaukarwar da Yesu ya yi lokacin da ya shiga daji domin yin addu'a tare da yin azumin kwana 40 kafin a gicciye shi.

Lokaci ne na neman yafiya wanda a lokacin kirsitoci ke bikin tunawa da gicciye Yesu a bikin Easter wanda ake yi a ƙarshen azumin na Lent.

... da kuma na musulmi

...

Asalin hoton, Getty Images

Ramadan shi ne wata na tara a kalandar musulunci. Wata ne mai muhimmanci a Musulunci.

A watan ne al'ummar musulmi suka yi imanin an saukar da ayoyin farko na Al Qur'ani mai tsarki wanda aka saukar wa Annabi Muhammad SAW.

A lokacin ne, aka umarci musulmi su yi azumi su kuma bayar da sadaka su kyautata wa juna su kuma kasance masu haƙuri tare da ƙarfafa kusancinsu da Allah.

Abubuwan duba tsakanin Ramadan da Lent

Azumi da kamewa:

Azumi ibada ce da ake yi a duka addinan, duk da cewa sun bambanta. Lokacin lent, kiristoci na yin azumi ta hanyar kamewa daga cin nama a ranar Juma'a da kuma taƙaita cin abinci na tsawon kwana 40. Hakazalika, a lokacin Ramadan, musulmi na kamewa daga ci da sha da shan taba da kuma saduwar aure daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana.

Duƙufa da ibada:

A lokutan azumin duka ɓangaren, ana so a duƙufa wajen yin addu'oi da neman yafiya. Mabiya addinan suna ƙara yin kusanci da ubangiji tare da neman yafiyarsa da tsarkake zukatansu.

Bayar da sadaƙa:

Lokacin Lent da Ramadan, ana jaddada muhimmancin bayar da sadaƙa da kuma kyautata wa waɗanda ba su da hali. Ana so mai azumi ya tausasa wa masu buƙata, lamarin da zai ƙara ƙarfafa kusanci a tsakanin al'umma da kuma haɗin kai.

Yadda Ramadan da Lent suka bambanta?

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsawon lokacin yin su:

Ana azumin Lent na tsawon kwana 40 inda ake farawa a ranar Ash Wednesday a kuma ƙare a ranar bikin Easter Sunday. Kiristoci ba su azumi ranar Lahadi. A ɗaya ɓangaren, musulmi na azumtar kwanaki ko dai 29 ko 30 - ya danganta da kamawar sabon wata.

Yanayin azumin:

Duk da cewa duka addinan sun umarci yin azumi, yadda ake yin sa ya bambanta. Azumi a watan Ramadan yana daga cikin rukunan musulunci biyar, da rayuwar duk wani musulmi ta ginu a kai.

Sauran rukunan su ne imani da yin sallah sau biyar a rana da bayar da zakkah da kuma sauke farali (Hajji) idan mutum na da hali.

Azumin Ramadan na sa mutane su ƙara kusancinsu da Allah.

Musulmi na cin abinci sau ɗaya a rana lokacin sahur kafin ketowar alfijir.

Da rana kuma, suna kamewa daga ci da sha har da ruwa da saduwa har sai rana ta faɗi, lokacin da suke buɗe baki.

Sai dai, akwai wasu musulmin da aka ɗauke wa azumin. Kamar mata masu juna biyu ko shayarwa da mata masu jinin al'ada da marasa lafiya ko waɗanda azumin zai iya shafar lafiyarsu da kuma matafiya. Amma bayan azumin, za su rama adadin azumin da suka sha ko kuma su ciyar.

A lokacin azumin Lent kuwa, kiristoci na yin addu'oi. Azumin ya zama dole ne kan kiristoci a ranar Ash Wednesday da kuma Good Friday. Masu azumin su na iya cin abinci sau ɗaya a rana.

Bayan ranakun Ash Wednesday da Good Friday, dole mutum ya kame a duk ranar Juma'a. Dokar kamewar ta haramta cin nama ban da kifi da sauran dabbobi da ake iya cin namansu.

A sauran ranakun Lent din, kirista na iya yin sauran nau'ikan ibada kamar karanta littafin Injila da zuwa taron addu'oi da bayar da sadaƙa da ziyartar marasa lafiya da fursunoni da bai wa talakawa sadaƙa da kuma koyar da ƙa'idojin addinin kirista.

Muhimmancinsu:

Lokutan ibadar biyu na da ma'anoninsu a wajen mabiya addinan. Lent na tunawa da kwanaki 40 na azumin da Yesu ya yi cikin daji da kuma shirya mabiya domin bikin ranar Easter.

“An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suka gaba ce ku, domin ku yi imani" kamar yadda yake cikin Al-Qur'ani Sura ta biyu, aya ta 183 kuma a watan ne aka saukar wa Annabi Muhammad SAW Al Qur'ani: "A watan Ramadan aka saukar da Qur'ani. Dokoki ne da ke yi wa ɗan’adan jagora a rayuwa" Qur'an 2/185)