Mai doya da 'yan makaranta na cikin hotunan Afrika na wannan makon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yar wasan sululun ƙanƙara daga Kenya Sabrina Simader a ranar Laraba A Meribel na Faransa inda ake wasan duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani matashi a ranar Asabar yayin bikin sabuwar shekarar Lunar a birnin Johannesburg na Afrika Ta Kudu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai wannan rana, wasu mata a birnin Durban na Afrika Ta Kudu suna bikin Thaipoosam Kavady na mabiya addinin Hindu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, wani yaro a kan cinyar mahaifiyarsa ɗauke da sarƙar wuya ta Kirista lokacin da mabiya Katolika suka taru a wani wajen suna jiran zuwa Fafaroma Francis

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu yara da aka je da su ziyara ke nan a Sudan ta Kudu... wasu na zaman jiran gudanar da addu'o'in zaman lafiya ga ƙasar da take fuskantar rikice-rikice.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mabiya addinin Kirista a Burkina Faso a wani ƙauye da ke gefen babban birnin ƙasar Ouagadougou domin yin addua a ranar Lahadi, inda wasu yara suka ɗauki hoto a jikin wani zaben coci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban masu ziyara ne suka halarci wajen bauta na Yagma, inda wannan limamin cocin ya ja ragamar dunadar da addu'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mabiya addinin Kirista na addu'a a wajen Yagma a Burkina Fasoa ranar Lahadi 5 ga watan Fabirairu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A makociyar ƙasar Ivory Coast a ranar Juma'a, wani malami na rubutu a kan allo a wata makarantar Islamiyya da ke birnin Abidjan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai wannan rana wasu 'yan damben gargajiya a Senegal da yamma suna gasar mutum biyu a filin wasa na ƙasar da ke Dakar b

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum mai sayar da doya a birnin Legas a Najeriya yana jiran masu saya a gefen titi a ranar Laraba.