Yadda za ku kare yaranku daga cutuka bayan komawa hutun makaranta

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ɗalibai ke komawa makaranta a faɗin Najeriya bayan hutun ƙarshen zango da ƙarshen shekara, yana da kyau iyaye da malamai da kuma makarantu su kula matuƙa da kuma yin taka-tsantsan da lafiyar ɗalibai musamman idan aka yi la'akari da lokaci ne da cutuka suka fi saurin yaduwa a tsakann al'umma.
A lokacin hunturu ana samun rikiɗewar yanayi inda ake samun sanyi da kuma ƙaruwar kaɗawar iska.
Dalilin haka ne wasu kan yi fama da rashin lafiya, musamman ma yara.
A halin da ake ciki a yanzu inda iska ke kaɗawa, cutukan da ke iya bin iska kan yaɗu sannan su bazu tsakanin al'umma.
Hakan ne ya sanya BBC ta tattauna da wasu likitoci da ƙwararrun malaman makaranta domin jin matakan da suka kamata iyaye da malamai su ɗauka domin kare lafiyar ƴan makaranta daga kamuwa da waɗannan cututtuka da kuma kasancewarsu cikin ƙoshin lafiya.
Cutukan da suka fi saurin yaɗuwa tsakanin yara

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Lawal Attahiru, wani babban likitan yara a Abuja ya ce cutukan da suka fi yaɗuwa tsakanin yara ƴan makaranta su ne wadanda iska ke yaɗawa da kuma waɗanda ke yaɗuwa ta hanyar cuɗanya.
Likitan ya ce cutukan su ne:
- Mura
- Tari
- Ciwon ido
- Amai da gudawa
- Cutukan fata
Yadda za a kare yara daga kamuwa da cutuka

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Attahiru ya bayyana cewa wajibi ne ɓangarori biyu da ke da hannu wajen ilimin yaran su ɗauki matakai domin hana yaɗuwar cutukan.
Wato akwai rawar da iyaye za su taka, sannan akwai rawar da hukumomin makarantu za su taka.
Matakan da iyaye za su ɗauka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Aliyu, ƙwararren likitan yara a asibitin Aminu Kano ya bayyana wa BBC matakan da iyaye za su iya ɗauka don hana yaransu kamuwa da cututtakan ko kuma yaɗa su.
- Kiyaye tsaftar hannu
Yana da kyau iyaye su koya wa ƴaƴansu tsaftar hannu. Tsaftace hannu hanya ce mafi inganci da aka tabbatar take hana yaɗuwar cuta, in ji dakta Aliyu.
Akwai buƙatar a koya wa yara wanke hannu kafin cin abinci da bayan gama ci, da bayan fitowa daga ban-ɗaki, da kuma bayan gama wasa. Sannan ya kamata a koya musu amfani da sanadarin tsaftace hannu na 'sanitizer'.
- Kula da abincin yara
Yana da kyau a guji bai wa yara abincin da ya kwana musamman idan za su ne da sanyi ba tare da an ɗunɗuma ba.
Haka nan a tsaftace mazubin abincin tare da tabbatar da cewa an rufe shi domin hana ƙwayoyin da ke haifar da cutuka ko ƙwari faɗawa.
- Amfani da takunkumi
Ya kamata a tilasta wa yara amfani da takunkumi musamman in aka samu ɓarkewar cutar da ka iya yaɗuwa ta iska.
Rufe baki ko hanci lokacin tari ko atishawa
Yana da kyau iyaye su koya wa yaransu amfani da ƙwalle ko
- Dakatar da zuwa makaranta
Domin hana yaɗa cuta, yana da kyau iyaye su hana duk yaron da aka lura ya kamu da cutar da ke iya yaɗuwa zuwa makaranta.
Idan yaro yana fama da cututtakan da suka shafi fata kamar ƙyanda da faran-kama da baƙon-dauro da kuma sauransu, yana da kyau a dakatar da su daga zuwa makaranta har sai sun warke
Hakan zai hana shi yaɗa cutar ga sauran ɗalibai ƴan'uwansa a lokacin da suka yi cuɗany a wuri guda.
- Zuwa asibiti
Idan aka lura cewa cutar ta yi tsanani ya kamata iyaye su kai yaro asibiti domin samun magani. Kuma kada a bari ya koma makaranta har sai ya warke daga cutar.
Wani masani kan lafiyar yara M.B Abubakar ya kuma bai wa iyaye shawarwari yadda za su inganta lafiyar yaransu kamar haka:
- Tabbatar da cewa yara sun yi bacci kan lokaci
- A rage yawan lokacin da yara ke kwashewa suna kallon talabijin da wasannin kwamfuta
- A tabbatar suna cin abinci mai lafiya
- A tabbatar suna shan ruwa sosai
- A rage yawan kayan maƙulace da suke ci
- A tabbatar suna samun hutu yadda ya kamata
Matakan da suka kamata makaranta ta ɗauka

Asalin hoton, Getty Images
- Samar da wurin wanke hannu
Dakta Attahiru ya bayyana cewa ya kamata makarantu su samar da wuraren wanke hannu ga yara, ta yadda za su wanke hannuwansu lokaci-lokaci domin gudun kamuwa da cutuka.
- Tabbatar da yara na wanke hannu
Wajibi ne makarantu su tabbatar da dokar wanke hannu tsakanin ɗalibai a makaranta.
A tabbatar ɗalibai sun wanke hannu bayan sun yi wasa da kafin cin abinci da kuma bayan cin abinci.
- Tsaftace muhallin makaranta
Ya kamata hukumar makaranta ta tabbatar da tsaftace ajujuwa da harabar makaranta domin guje wa yaɗuwar ƙwayoyin cuta.
Barin shara a makaranta zai gayyato dabbobi da ƙwari kamar ɓera da ƙudaje zuwa cikin ajujuwa da harabar makaranta.
- Hana malamai marasa lafiya mu'amala da yara
Bai kamata a bar malamin da ke nuna alamar wata cuta mai yaɗuwa ya koyar ko kuma ya kula da ɗalibai ba.
Idan ya kasance ma'aikaci ya zo makaranta ba shi da lafiya, yana mura ko tari ko wata cuta makamanciyar haka sai a ba shi sarari ya yi nesa da yaran ko kuma ya zauna a gida har sai ya warke. Ta haka sai ya kasance an kare yaɗuwar cutar a tsakaninsu.
Dakta Attahiru ya ce ma'aikaco ko malamain da ya zama dole ya je aikin kuma yana fama da mura sai ya yi amfani da takunkumin kariya tare da yin nesa-nesa da ɗalibai da sauran ma'aikata.
- Hana yara marasa lafiya zuwa makaranta
Dakta Attahiru ya ce yana da kyau makarantu su kafa doka tare da tabbatar da cewa ana amfani da ita wajen hana yara da ke fama da rashin lafiya zuwa makaranta domin kare yaɗa cuta zuwa ga sauran yara.











