Barca ta zama ta farko da ta kai kwata fainal a Champions League

Barcelona

Asalin hoton, Getty

Lokacin karatu: Minti 2

Matashin ɗan wasa Lamine Yamal ya haskaka da ta kai Barcelona ta doke Benfica ta kai kwata fainal a Champions League ranar Talata.

Mai shekara 17 ya bai wa Raphinha ƙwallon farko da ya zura a raga, sannan shi da kansa ya kara na biyu da kuma Raphinha da ya kara na uku na biyu a wasan.

Minti biyu tsakani da Barcelona ta ci ƙwallon farko, Nicolas Otamendi ya farkewa Benfica a wasan da aka tashi 3-1.

Kenan ƙungiyar Sifaniya ta kai zagayen gaba da cin 4-1 gida da waje.

Ƙwallo biyun da Raphinha ya ci ya zama yana da hannu a 16 a raga a Champions League a kakar nan.

Lionel Messi ne kan gaba a Barcelona da ya ci ƙwallo 14 ya bayar da biyar aka zura a raga a 2011/12, fiye da Raphinha mai 11 da ya bayar da biyar aka zura a raga.

Da wannan sakamakon Barcelona za ta fuskanci duk wadda ta yi nasara tsakanin Borussia Dortmund ko Lille a ƙwata fainal.

Yamal ya ci gaba da kafa tarihi

Lamine Yamal ya ci gaba da kafa tarihi a fannin tamaula a duniya

Matashin ya taimakawa Sifaniya ta lashe kofin nahiyar Turai a bara a Jamus, tun daga nan sai kara yin bajinta yake a kakar nan.

Ƙwallon da ya ci da wanda ya bayar aka zura a raga ya zama na 28 a kakar bana, ba wai ƙwallon da yake ci bane, irin salon da yake taka leda abin burgewa ne.

Yanzu haka matashin ya kusan ci wa tawaga da ƙungiya ƙwallo 60.

Haka kuma rawar da Yamal ya taka a ranar Talata a karawa da Benfica ya kafa tarihi a matakin mai shekara 17 da kwana 241 da ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura a raga a wasan Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barcelona ta kara da Benfica a wasa na biyu zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Talata a Sifaniya ta kai zagayen kwata fainal.

A wasan farko a Portugal an bai wa ɗan wasan Barcelona, Pau Cubarsi jan kati, amma hakan bai hana Raphinha zura ƙwallo ba a ragar Benfica.

Benfica ta kasa yin nasara a wasa biyar baya da ta je Barcelona, wadda rabon da ƙungiyar Portugal ta doke ta a gida tun bayan 1952.

Har yanzu ba a doke Barcelona ba a dukkan karawar da ta yi a shekarar 2025.

Barcelona za ta buga wasan na ranar Talata tare da alhinin mutuwar likitan ƙungiyar, Carles Minarro, kafin wasa da Osasuna, wanda ya zama kwantai a La Liga.

Marc-Andre ter Stegen da Marc Bernal suna jinya har bayan kakar nan, har yanzu Andreas Christensen bai murmure ba.

Haka kuma Barcelona ta yi wasan ba tare da Pau Cubarsi ba, wanda aka yi wa jan kati a wasan farko a Portugal.

Benfica na fama da masu jinya da suka haɗa da Alexander Bah da Manu Silva da Tiago Gouveia da tsohon ɗan wasan Real Madrid, Angel Di Maria kan wasan.

Alvaro Carreras yana hutun hukuncin katin gargadi da yawa da ya karɓa, yayin da Bruma bai cancacji buga fafatawar ba.

Ƴan wasan Barcelona da suka fuskanci Benfica:

Balde, Araujo, Iñigo, Gavi, Ferran, Pedri, Lewandowski, Ansu, Raphinha, Iñaki, Pablo Torre, Fermín, M. Casadó da Pau Víctor.

Sauran sun haɗa da Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczesny, Kochen, H. Fort da kuma Gerard Martin.