Hukunce-hukuncen shari'o'in da suka haɗa kan 'yan siyasar Najeriya

Nigerian governors

Asalin hoton, BABAJIDE/OTTI/ABBA/DARE/SOCIAL MEDIA

Ranar Juma'a 12 ga watan Janairun 2023, ta kasance muhimmiyar rana, wadda Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunce-hukuncen shari'o'in zaɓen gwamnoni guda takwas.

Hukunce-hukunce ne waɗanda ga dukkan alamu suka haɗa kan 'yan siyasar ƙasar da sake farfaɗowa da ƙarfafa fatansu ga mulkin dimokraɗiyya.

Jihohin da hukunce-hukuncen suka shafa sun haɗar da na kudanci da arewacin ƙasar kuma daga jam'iyyun siyasa daban-daban.

Babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP wadda gwamnoninta uku suka yi nasara a kotun ƙolin ta ce "Ɓarkewar ruguntsumin murna a faɗin jihohin Bauchi da Filato da kuma Zamfara, wata manuniya cewa hukunce-hukuncen sun yi daidai da tsammanin 'yan Najeriya wajen bin kadin adalci da mulkin doka da kuma zurfafa dimokraɗiyyar tsarin mulki a ƙasarmu".

Fitattun 'yan siyasar ƙasar ne ke ci gaba da mayar da martani ga hukunce-hukuncen.

Nasarar ranar Juma'a

  • Dauda Lawan Dare na Zamfara - PDP
  • Caleb Mutfwang na Filato - PDP
  • Bala Mohammed na Bauchi - PDP
  • Abba Kabiru Yusuf na Kano - NNPP
  • Alex Otti na Abia - LP
  • Francis Nwifuru na Ebonyi - APC
  • Sanwo-Olu na Legas - APC
  • Bassey Otu na Cross River - APC

PDP

PDP a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan hukunce-hukuncen kotun ƙoli ta ce tabbatar da zaɓen gwamnonin da kotu ta yi, muhimmiyar nasara ga dimokraɗiyya da ƙudurin da al'ummar Bauchi da Filato da kuma Zamfara suka bayyana a yunƙurinsu na samun shugabanci mai manufa da kuma shugabanci nagari.

Ta ce game da jihar Filato, PDP tana yaba wa ƙarfin halin Kotun Ƙoli wajen tabbatar da ƙudurin jama'a da kuma nuna cewa tabbas ɓangaren shari'a shi ne tudun ƙarshe ga talaka.

Ta ƙra da cewa hukuncin ya zo ne a matsayin wani hatimi ga nasarar da jajirtattun mata da matasa da ɗaukacin al'ummar jihar suka nuna wajen bayyana ƙudurinsu na 'yantar da jiharsu.

APC

Ita ma jam'iyyar APC mai mulki, ta ce hukunce-hukuncen sun samar da wani tabbaci mai ƙarfi ga ikon hukuma da jajircewa da kuma 'yancin cin gashin kai na ɓangaren shari'a.

Ta ce ita kullum matsayinta shi ne a bar ɓangaren shari'a, shi kaɗai ya aiwatar da muhimmin aikinsa na warware rikice-rikice ciki har da rikicin zaɓe kamar yadda tsarin mulki ya ɗora masa alhaki.

Sai dai ta ce hukunce-hukuncen za su zama gwasale manyan 'yan adawa ne da suka fito suka ci zarafi tare da ƙasƙantar da kotunan ƙasar lokacin da suka yanke hukunce-hukunce irin waɗannan, da ba su yi musu daɗi ba.

APC ta goranta wa PDP cewa kamata ya yi jam'iyyar adawan ta fito ta nemi afuwa a kan haka.

APC Document

Asalin hoton, APC/X

Atiku Abubakar

Jagoran adawar ƙasar kuwa ya ce hukuncin kotun ƙolin wata gagarumar nasara ce ga al'ummar Bauchi da Filato da Akwa Ibom da kuma jihar Zamfara kuma babu ko tantama wata galaba ce ga dimokraɗiyyar tsarin mulki.

Atiku Abubakar ya kuma ce yana taya murna da jinjina ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP, saboda nasarar kotun da ya samu abar yabawa.

Ya ce wannan lokaci ne da ya bayar da wata kyakkyawar dama ta sake jaddada ƙudurina na tunanin cewa dunƙulewar 'yan adawa abu ne mai muhimmanci don ƙarfafa dimokraɗiyyar Najeriya.

Ya ƙara da cewa hukuncin Kotun Ƙolin zai tabbatar da ci gaba da samun shugabanci mai matuƙar ingancin da a cewarsa PDP ta kafa a waɗannan jihohi.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Babajide Sanwo-olu

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos, yana cikin gwamnoni guda takawas da Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar zaɓensu ranar Juma'a, kuma bayan hukuncin ya wallafa sanarwa a shafinsa.

Yana cewa bayan wata ganawa da Ƙungiyar Gwamnonin APC a fadar shugaban ƙasa, Shugaba Bola Ahmed Tunubu ya taya shi murna bisa nasarar da ya samu.

Tinubu and Progressive governors

Asalin hoton, BABAJIDE SANWO-OLU/FACEBOOK

Bayanan hoto, Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar zaɓen Sanwo-Olu ne bayan ta kori ƙararrakin 'yan takarar LP da na PDP.

Gwamnan na Lagos ya ƙara da cewa kamar yadda a ko yaushe nake faɗa, "babu wanda ya yi nasara kuma babu wanda aka kayar".

Ya kuma ce yana gayyatar waɗanda har yanzu suke kan katanga su sauko su shiga jirgin shugabanci mai ra'ayin kawo ci gaba. A cewarsa, yana tafiyar da gwamnati wadda ƙofarta a buɗe take, don haka kada wani ya yi ƙorafin cewa an tattare damar ba da gudunmawar tunani.

Ya yi fatan ci gaba da aiki tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat don gina Lagos da za ta bunƙasa kuma ta samu ci gaba tare da ɗaga martabar kowanne mazaunin jihar.

Bukola Saraki

Shi ma tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki ya ce wannan mataki na tabbatar da nasara da Kotun Ƙoli ta yi wa zaɓen wasu gwamnonin jam'iyyarsu ta PDP, wata shaida ce tsarin dimokraɗiyya shi ne ginshiƙi wajen gudanar da al'amuran ƙasar.

Ya yi fatan alheri ga gwamnonin na jihohin Akwa Ibom da Bauchi da Zamfara da kuma Filato.

Haka zalika, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murna bisa nasarar da ya samu shari'ar da Kotun Ƙoli ta yanke hukunci.

Ya ce nasarar tasa a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP ta ƙara tabbatar da gawurtaccen ruhin adawa da kuma ƙarfin juriya na tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.

Caleb Muftwang

Caleb Mutfwang

Asalin hoton, Caleb Mutfwang/Facebook

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang a jawabinsa kan nasarar da ya samu a shari'ar Kotun Ƙoli, ya ce al'ummar jihar Filato ne suka damƙa masa ikon ya mulke su, kuma ba zai ba su kunya ba.

Ya jinjinawa Kotun Ƙolin Najeriya saboda abin da ya kira tabbatar da mulkin doka da ikon jama'a na fitar da wanda zai mulke su. Ya ce alƙalan kotun sun nuna ƙarfin gwiwa da ƙima wajen zartar da hukuncin adalci ga talakan Najeriya.

Caleb Mutfwang ya kuma ce yana yaba wa Bola Tinubu saboda shugabancinsa na dimokraɗiyya da mutunta ɓangaren shari'a. A cewarsa, Tinubu ya tabbata dattijon ƙasa na haƙiƙa kuma garkuwan ƙuri'un jama'a.

Gbadebo Rhodes-Vivour

Sai dai a ɓangare ɗaya, waɗanda hukuncin bai yi wa daɗi ba, kamar ɗan takarar gwamnan Lagos a zaɓen 2023 na jam'iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour sun tofa nasu albarkacin baki.

Ya ce Kotun Ƙolin ta dasa wani ɗan ba: (cewa) gwamna ko shugaban ƙasa na iya mallakar damar zama ɗan ƙasa ga ɗumbin ƙasashe saɓanin Najeriya kuma duk da haka ya zama babban jami'in tsaro na Lagos ko kuma Najeriya.

Ya ce ko da yake, ya miƙa wuya ga wannan hukunci mai ban mamaki da Kotun Ƙoli ta yanke, amma ya damu kan abin da wannan mataki ke nufi ga makomar al'ummar ƙasar ta gaba, wadda za a samu shugabanni da ke da rashin tsayar da zuciyarsu wuri ɗaya.

Nentewe Goshwe

Shi ma ɗan takarar gwamnan Filato na jam'iyyar APC a zaɓen 2023 Nentewe Goshwe ya ce daga bisani an kai ƙarshe a tsarin babban zaɓen 2023, kuma sun karɓi hukuncin Kotun Ƙoli cikin ƙasƙas da kai da kuma godiya ga Allah.

Da yake yaba wa jajircewar magoya bayansa, ya kuma taya murna ga Gwamna Caleb Mutfwang bisa nasarar da kotu ta tabbatar masa.

Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar Filato da ɗumbin masu fatan alheri su tabbatar da zaman lafiya a jihar ta tsakiyar Najeriya.

Aisha Yesufu

A Nigerian female activist

Asalin hoton, AISHA YESUFU/X

Yayin da fitacciyar 'yar gwagwarmayar nan ta Najeriya, Aisha Yesufu ta wallafa nata saƙon a shafinta na X, cewa Kotun Ƙoli ta yi daidai kan zaɓen gwamnan Kano.

Ta ce NNPP ta ci zaɓe, kuma da ma kamata ya yi a ko da yaushe a bar damar ikon zaɓen mai mulki a hannun jama'a.