...Daga Bakin Mai Ita tare da Mustapha Ibrahim

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Lokacin karatu: Minti 1

Almustapha Ibrahim haifaffen jihar Kastina ne, wanda ya shahara a fagen waƙa da sunan El-Musty.

Shi ne ya rera waƙar nan ta siyasa mai suna "Ba Mu Babu Ku".

Ya yi karatun firamamre da sakandare, har zuwa matakin kwaleji a jiharsa ta Katsina.

Ya fara waƙa a shekarar 2010, inda ya ce mawaƙa Tasiu Unguwa Uku da Naziru Sarkin Waƙa ne suka fi yin tasiri a rayuwarsa.