PSG ta lashe Ligue 1 sauran wasa shida a kare kakar bana

PSG

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Paris St Germain ta yi nasarar lashe Ligue 1 na bana, bayan da ta yi nasara a kan Angers 1-0 ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta Faransa.

Matashin ɗan wasanta Desire Doure ne ya cin ƙwallon da ta kai PSG ta lashe kofi na huɗu a jere, kuma saura wasa shida-shida a kare kakar bana.

Tun kan karawar ƙungiyar da Luis Enrique ke jan ragana na bukatar yin canjaras ta lashe kofin kakar nan, bayan da Monaco ke mataki na biyu.

Wannan shi ne karo na uku da aka ɗauki Ligue 1 da saura wasanni da yawa kan a karkare gasar tamaula ta Faransa.

PSG ta yi wannan bajintar a karon farko karkashin Laurent Blanc, saura karawa takwas-tkwas a kammala kakar 2016.

Sai tun kafin nan Lyon ta ɗauki Ligue 1, saura a gama wasa shida-shida a Ligue 1 a kakar 2007.

Wannan shi ne Ligue 1 na 11 da PSG ta ci a kaka 13 baya, kuma kofi na 13 jimilla a dukkan gasa.