Abu biyar da majalisar tattalin arziƙin Najeriya ta tattauna a kai

...

Asalin hoton, Presidency

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Alhamis 31 ga watan Oktoba ne majalisar ƙoli ta tattalin arziƙin Najeriya ta yi zamanta karo na 145 a fadar shugaban ƙasa, inda ta tattauna da cimma wasu batutuwa muhimmai.

Majalisar wadda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke jagoranta mai ƙunshe da gwamnonin ƙasar 36 ta tattauna batutuwa da dama kamar yadda takardar bayan taron mai ɗauke da sa-hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa mataimakin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Stanley Nwokocha, ta zayyana.

BBC ta tsakuro guda biyar daga ciki waɗanda suka fi ɗaukar hankalin ƴan Najeriya.

1) Janye ƙudirin harajin VAT

Majalisar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta janye batun ƙudirin yi wa dokar harajin kaya gyaran fuska daga Majalisar Dokokin ƙasar domin bayar da isasshen lokaci na tattaunawa da tuntuɓar juna a tsakanin masu ruwa da tsaki kan harajin.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan shugaban kwamitin shugaban ƙasa na musamman kan tsare-tsare da yi wa haraji garambawul, Mista Taiwo Oyedele ya gabatar da jawabi game da tsare-tsaren da suke yi, inda majalisar ta ce akwai buƙatar a samu ƙarin lokaci domin tattaunawa tare da fahimtar juna.

2) Faɗaɗa wuraren samar da wutar lantarki a ƙasa

Shugaban majalisar kuma mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya ce za su ɗauki matakin rarraba wuta a faɗin ƙasar maimakon a wani ɓangare guda domin tabbatar da ba a sake samun irin katsewar lantarkin da aka fuskanta ba a kwanankin baya a arewacin ba.

Sanata Kashim Shettima ya ce mata lissafa hanyoyin cimma hakan da suka haɗa da kafa ƙananan tashoshin samar da wutar da amfani da hasken rana da iska, inda kuma ya jadda buƙatar ƙaddamar da tsarin samar da wuta na NESIP.

3) Yawan tallafin da gwamnati ta bai wa ƴan Najeriya

Ministan kuɗi na Najeriya wanda ya gabarta wa da majalisar irin nasarorin da suka samu a tsawon shekara guda da ƴan watanni ya lissafa jerin talalfi ga ƴan Najeriya kamar haka:

Gwamnati ta bai wa ƴan Najeriya miliyan 25 tallafin kuɗi naira 25,000 ta hanyar aikewa ta asusunsu.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta bayar da rance ga masu harkokin intanet da samar da wutar lantarki da noma da kiwo da lafiya da kuma iskar gas.

4) Gargaɗi ga masu ɓoye dalar Amurka

Ministan na kuɗi na Njeriya, Wale Edun ya gargaɗi masu ɓoye dalar Amurka, inda ya ce bisa sabon tsarin gwamnati an ba su wa'adin watanni tara da su fito da dalolin zuwa bankunan Najeriya.

Ministan ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifin ƙin fito da dalolin lokacin da wa'adin ya ƙare ta za a hukunta shi daidai da laifinsa.

5) Asarar da Najeriya ta yi sakamakon ambaliya

Majalisar ta fitar da alƙaluman asarar da Najeriya ta yi na rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliyar ruwa da ƙasar ta fuskanta a damunar bana.

Majalisar ta ce ambaliyar ta shafi jihohi 34, da ƙananan hukumomi 217, inda ta shafin mutane fiye da miliyan 1.3.

Minsitan albarkatun ruwa wanda ya bayyana hakan, Farfesa Joseph Utsev ya ce ambaliyar ta ɗaiɗaita mutum 740,743 sannan mutum 321 sun mutu sannan kuma an yi asarar gonaki da gidaje masu yawa.