Fitsari a tsaye ko a tsugune: Wanne ne ya fi kyau ga lafiyar maza?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 3
A zaune ko a tsaye? Wannan ce tambayar da ake yawaita yi a muhawarar yadda ya kamata maza su dinga yin fitsari.
Yayin da babu wata cikakkiyar hujja a likitance cewa zaman yana da wani amfani ga lafiya, amma an amince ita ce hanya mafi tsafta ta yin fitsari.
"Babu wata hanyar da ta fi wata wajen yin fitsari, kawai ya danganta ne ga abin da mutum ya fi so," in ji Dr Mary Garthwaite, shugabar wata gidauniya a Birtaniya mai suna Urology Foundation.
"Amma kuma zama ya fi tsafta idan dai banɗakin mai tsafta ne."
Dr Garthwaite ta ƙara da cewa zaman zai fi kyau ga mutanen da ke da larurar wajen motsa jiki, ko kuma masu tashi tsakar dare domin yin fitsari.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike na 2014 da ake yawan ambatowa da Jami'ar Leiden ta gudanar da a Netherlands ya nazarci yadda tsayuwar jiki ke shafar fitar fitsari da kuma saurin fitarsa daga jikin mutum.
Sun daddale cewa zama ya fi fitar da fitsari cikin sauri kuma gaba ɗaya ga mazan da ke fama da kumburin bayan mafitsara, amma kuma "babu bambanci" tsakanin masu lafiya.
Akasari, yin fitsari a tsaye ba sabon abu ba ne a wajen maza. Amma kuma yi a tsaye na ƙara yawan haɗarin fallatsi, wanda wasu da yawa suka tsana.
Sannan ba wai muna magana ne kan digo-ɗigon fitsari a mazaunin bahaya ko a dandariyar ƙasa ba.
Wasu masu bincike a Amurka sun gano a 2013 cewa fallatsin fitsari "kan watsu a wurare masu nisa da faɗi", abin da ke nufin abubuwan da ke kusa - kamar burushin goge baki - fitsarin na hawa kansu.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu al'ummomin kan umarci maza su dinga tsugunawa ko zama idan za su yi fitsari, musamman tsakanin Musulmi. Amma dai wasu sun fi son yin a tsayen saboda haka suka saba.
A 2023, cibiyar YouGov ta gudanar da wani bincike a ƙasashe 13 kan zaɓin maza wajen yin fitsari.
Cibiyar ta gano babban bambanci hatta a nahiya ɗaya: yayin da kashi 40 cikin 100 na mazan Jamus suka ce suna zama duk lokacin da za su yi fitsari, kashi 10 ne kacal suke yi a tsaye kodayaushe. A Birtaniya kuma, 9 da kuma 33 ne a kowane ɓangare.
Da alama masu yin fitsari a zaune sun fi yawa a Jamus, ƙasar da ake kiran masu yin fitsari a zaune Sitzpinkler wadda ake siffanatawa a matsayin ragon maza. A Brazil, akan faɗi wata magana cewa "fitsari a zaune na mata ne da kuma kwaɗi".
Ko akwai buƙatar sai mazaje sun tashi tsaye sun yaƙi asalin halittar ɗan'adam kafin su iya sauya yadda suke yin fitsari? Dr Robert Dunbar na Jami'ar Oxford ƙwararre ne a fannin asalin halittar ɗan'adam kuma ba shi ganin akwai buƙatar hakan.
"Babu wata hujja [a nazarin asalin halitta] game da dalilin da ya sa maza ke fitsari a tsaye," in ji shi.
"Magana ta gaskiya wasu kawai sun fi in dadin yin fitsari a tsaye, wasu kuma a zaune ko tsugune," a cewar Dr Garthwaite.
Idan ba a samu wata takamaimiyar shawarar likitoci ba, hanyar yin fitsari za ta ci gaba da zama a buɗe ga maza, sai dai fa idan 'yan'uwansu mata sun matsa musu su dinga zama ko kuma idan an kafe sanarwar su yi a zaune a bangon banɗaki - kamar a Jamus.
Amma dai idan ka zaɓi ka yi a tsaye, to zai yi kyau ka tabbatar ka saita inda ya kamata ya shiga.











