Mateta zai tafi AC Milan, Carrick na son dawo da Rashford a Man Utd

Asalin hoton, @FabrizioRomano

Lokacin karatu: Minti 1

Jean-Philippe Mateta ya amince da yarjejeniya da AC Milan har zuwa 2030, Kocin Crystal Palace Oliver Glasner ba zai bar ɗanwasan gaban na Faransa ya tafi ba har sai ya samu wanda zai maye gurbinsa. (Times - subscription)

Mateta na jiran tabbaci kafin ya tafi a diba lafiyarsa a AC Milan, amma Crystal Palace ke da wuka da nama. (Kaveh Solhekol)

Fulham ta taya Joe Willock kan fam miliyan 20 amma Newcastle United ta ƙi amincewa, har sai ta samu madadinsa. (Talksport)

Idan Michael Carrick ya ci gaba da aikin horar da Manchester United bayan kammala kaka, yana son dawo da Marcus Rashford, mai shekara 28, wanda ke taka leda a Barcelona a matsayin aro. (Telegraph - subscription)

Sunderland da Everton na son ɗanwasan gaba na Chelsea Tyrique George. Ƙungiyoyi daga Spain da Faransa da Italiya ma na ribibin ɗanwasan. (Sky Sports)

Sunderland ta yi wa Napoli tayin ɗanwasan Faransa Wilson Isidor. (Calciomercato - in Italian)

Tottenham da Leeds United na cikin ƙungiyoyin Premier da ke farautar ɗanwasan Colombia mai shekara 22 Jhon Duran, wanda ke taka leda a Fenerbahce a matsayin aro daga Al-Nassr. (Teamtalk)

Liverpool da Chelsea na tattaunawa da Rennes domin karɓo ɗanwasan baya Jeremy Jacquet. (Fabrizio Romano)

Chelsea na nazarin dawo da danwasan Senegal Mamadou Sarr wanda ta ba Strasbourg aro. (Sky Sports)