Mariani ne zai yi raflin wasan Dortmund da Barca a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Uefa ta sanar da naɗa Maurizio Mariani a matakin wanda zai yi alkalancin wasan Borussia Dortmund da Barcelona a Champions League ranar Talata.

Barcelona, wadda ta caskara Dortmund 4-0 a makon jiya, za ta je Jamus domin buga wasa na biyu zagayen kwata fainal a gasar zakarun Turai.

Raflin ɗan kasar Italiya, zai busa wasan Champions League na biyu a jere, shi ne ya yi rafli a karawar da Paris St German ta doke Aston Villa 3-1 a Faransa a makon jiya.

Haka kuma wani alkalin daga Italiya, Marco Di Bello, shi ne zai kula da na'urar da ke taimakawa alkalin wasan tamaula yanke hukunci wato VAR a wasan na Dortmund da Barcelona.

Haka kuma Daniele Bindoni da Alberto Tegoni za su yi aikin mataimakan Mariani, inda Simone Sozza zai yi jiran ko-ta-kwana, sai Daniele Doveri mataimakin VAR.

Mariani, mai shekara 43, ya yi rafli a wasa 16 a Serie A cikin kakar nan da busa karawa shida a Champions League da uku a Serie B.

Mariani ya yi alkalanci a wasan da Borussia Dortmund ta je ta doke Sevilla 4-1 a Champions League a 2022, yayin da wannan ne karon farko da zai yi rafli a karawar da ta haɗa da Barcelona.

Haka kuma a ranar ta Talata za a fafata tsakanin Inter Milan da Bayern Munich, inda Inter ta ci 2-1 a Jamus a makon jiya.

Duk wadda ta kai matakin gaba za ta fuskanci Barcelona a zagayen daf da karshe a Champions League da zarar ta Sifaniya ta yi waje da Dortmund.