Yadda Pele ya taɓa maƙalewa a Legas

Pele

Asalin hoton, Getty Images

Ɗaya daga cikin lokuta mafi firgitarwa da Pele ya fuskanta a rayuwarsa shi ne wata tafiya da ya yi zuwa birnin Legas na Najeriya a 1976.

Tafiya ce wadda kamfanin Pepsi ya ɗauki nauyi.

A daidai lokacin tasa ne wasu sojoji suka yi yunƙurin yi wa gwamnatin Janar Murtala Mohammed juyin mulki, inda aka kashe shugaban ƙasar duk da cewa juyin mulkin bai yi nasara ba.

Pele ya je Legas ne a watan Fabrairu domin buga wasan sada zumunta da kuma ƙaddamar da makarantun horas da ƙwallon ƙafa.

Kuma ba shi kaɗai ne mashahurin dan wasan duniya da ke a Legas ba a wannan lokaci, har da shahararren ɗan wasan tennis Arthur Ashe, wanda shi kuma yake buga wata gasa.

Pele ya maƙale a Legas bayan da aka rufe iyakokin Najeriya, kuma bai samu ficewa ba har sai lokacin da gwamnati ta buɗe iyakokin ƙasar.

A daidai wannan lokaci hukumomin Brazil sun bayar da shawarar a yi wa Pele shigar-burtu domin ya fice daga ƙasar.

Matsalolin iyali

Pele da ɗansa Edson Cholbi

Asalin hoton, Getty Images

Ana kallon Pele a matsayin kamilin mutum idan za a kwatanta shi da takwaransa wajen shuhurar ƙwallon ƙafa, Diego Maradona, to sai dai rayuwa tare da iyalansa na cike da ƙalubale.

Kotu ta yanke wa ɗansa na farko Edinho ɗaurin sama da shekara 12 bayan kama shi da laifin safarar miyagun ƙwayoyi da halasta kuɗin haram.

A wata tattaunawa da kafar yaɗa labaru ta Bleacher Report, Edinho ya bayyana mahaifin nasa a matsayin wanda ba ya bai wa iyalansa lokaci tun bayan da ya kwashe iyalin nasa zuwa New York, lokacin da yake buga wa ƙungiyar Cosmos wasa a tsakiyar shekarun 1970.

Ya ce mahaifin nasa ya yi watsi da matarsa Rosemeri dos Reis Cholbi jim kaɗan bayan isar sa Amurka.

Pele da matarsa Marcia Aoki

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga baya Pele ya sasanta da ɗan nasa, sai dai matsalar da ya fuskanta da babbar ɗiyarsa ta fi muni.

Ya ƙi amincewa da ita (Sandra Arantes do Nascimento), a matsayin ƴarsa duk kuwa da hukuncin kotu a shekarar 1996, wanda ya bayyana cewa ƴarsa ce halak-malak, bayan kwashe shekara biyar ana sharia’a.

An haifi Sandra ne a 1964 sanadiyyar alaƙar Pele da mai yi masa hidima.

Daga baya ta rubuta wani littafi da ta yi wa taken ‘The Daughter The King Didn't Want’, wato ‘Ɗiyar da aka samu ba da son ran sarki ba’.

Ta rasu a shekarar 2006 sanadiyyar cutar sankarar mama tana da shekara 42, kuma Pele bai halarci jana’izar ta ba, kuma ba ya ɗaukan ƴayanta biyu a matsayin jikokinsa.

Lokacin da ya kusa shekara 80 da haihuwa, Pele ya yi aure a karo na uku a shekarar 2016, inda ya auri wata ƴar kasuwa mai suna Marcia Aoki, mai shekara 42.

Tun a shekarun 1980 ne Pele da Aoki suka san juna, sai dai sun fara soyayya ne a 2010 lokacin da suka sake haɗuwa a birnin Sao Paulo bayan dogon lokaci.