Kotu ta yanke wa Dani Alves hukunci ɗaurin shekara huɗu

Wata kotu a Spain ta samu tsohon ɗan wasan Barcelona da Brazil Dani Alves da laifin yi wa wata mata fyaɗe a wani gidan rawa a birnin Barcelona.
An yanke masa zaman gidan yari na shekara huɗu da rabi.
Mai shekara 40 ɗin, na ɗaya daga cikin 'yan wasan kwallon da suka fi samun kyautuka a tarihi, ya musanta zargin cin zarafin da ake yi masa na lalata kan matar tun a ƙarshen watan Disambar 2022.
Lauyarsa ta nuna rashin gamsuwa da hukuncin kuma ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Lauyan wadda take ƙara ya yi maraba da wannan hukunci, yana cewa hakan yana tabbatar da abin da suke yaƙi akai a tsayar da gaskiya, kan wadanda aka zalunta.
Yayin da zai a miƙa ɗan wasan gidan yari na shekara hudu da rabi, kotun ta ce za a ƙara yi masa ɗaurin shekara biyar da za a riƙa bibiyar abin da yake yi.
Mai gabatar da ƙarar ya nemi a ɗaure shi na shekara tara.
A Spain, ana binciken duk wani iƙirarin fyade ƙarƙashin zargin cin zarafin lalata, kuma idan aka samu mutum da laifin akan yanke masa shekara 15 a gidan yari.
Matarsa Joana Sanz mai shekara 31, ta ce ya randa abin ya faru ya koma gida ne a buge.
Sai dai kotu ta ce buguwarsa ba za ta sauya masa halayyarsa ba.
Tun da fari ya musanta sanin matar da ta yi zarginsa amma dai daga baya ya ce ya santa sun haɗu a banɗaki amma dai babu abin da ya faru tsakaninsu.
Amma daga baya ya ƙara bayanin cewa sun yi wasu 'yan abubuwa da suka jiyar da junansu dai.
Alves ya buga wa Barcelona sama da wasanni 400, ya ci La Liga shida ya ci Champions uku. Kuma yana cikin tawagar Brazil da ta je gasar Kofin Duniya ta 2022.
Ya lashe kofina da yawa a lokacin da ya zauna a Sevilla da Juventus da kuma PSG, kuma shi ne ya fi buga wasa a Brazil, inda ya buga wasa 126.











