Manyan ƴan takara da ke neman maye gurbin Nasiru El-Rufai a jihar Kaduna

Hoton manyan ƴan takarar gwamna a Kaduna
Bayanan hoto, Manyan ƴan takarar gwamna a Kaduna

Zaɓen gwamna a jihar Kaduna da za a yi ranar 18 ga watan Maris ɗaya ne daga cikin zaɓukan da mutane ke dakon ganin yadda zai kaya la'akari da abubuwan da suka faru ta ɓangaren siyasa cikin shekarun baya-bayan nan.

Kaduna jiha ce da ke da muhimmanci a arewacin Najeriya, kuma ta taɓa zama babban birnin yankin a jamhuriya ta farko, abin da kuma ya sa hankalin mutane ke karkata ga al'amuran da suka shafi jihar.

A ranar 29 ga watan Mayu ne Gwamna Nasiru El-Rufai zai cika shekara takwas yana jagorantar jihar inda kuma zai miƙa ragama ga mutumin da al'ummar jihar za su zaɓa a matsayin wanda zai gaje shi.

A karon farko a zaɓen da aka yi a 2019, gwamna El-Rufai ya zaɓi musulma da ta mara masa baya, abin da kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta yi riƙo da shi ke nan a lokacin da jam'iyyar ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Ƴan takara 14 ne ke neman maye gurbin gwamna El-Rufai a zaɓen da ke tafe. BBC ta tattaro sunayen manyan ƴan takarar da tarihinsu.

Sanata Uba Sani - APC

Hoton Uba Sani

Asalin hoton, ubasanius/Twitter

Bayanan hoto, @ubasanius

Sanata Uba Sani ne ɗan takarar Jam'iyyar APC mai mulki kuma ɗaya daga cikin fitattun ƴan takara a zaɓen ranar Asabar.

Yana takarar tare da mataimakiyar gwamnan jihar ta yanzu, Hadiza Balarabe.

Ya yi fice ne bayan da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya naɗa shi a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin jama'a bayan da ya ci zaɓe a 1999.

An haifi Sanata Uba Sani ranar 31 ga watan Disamban 1970.

Ya yi karatun injiniya amma kuma a cikin siyasa ya tashi kasancewar danginsa sun yi suna a wannan ɓangare.

Ɗan takarar wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar dattawa, ya taɓa shan kaye bayan da ya yi rashin nasara a neman kujerar sanata ƙarƙashin PDP a 2011.

Yana kuma cikin ƴan takarar da BBC Hausa ta yi hira da su a muhawarar ƴan takarar gwamna a jihar Kaduna inda ya sha alwashin ɗorawa kan ayyukan gwamna Nasiru El-Rufai.

Jonathan Asake - LP

Jonathan Asake

Asalin hoton, Jonathan Asake

Jonathan Asake ne ɗan takarar Jam'iyyar Labour a zaɓen gwamnan na ranar Asabar.

Jonathan ya fito ne daga Kudancin Kaduna kuma tsohon ɗan majalisa ne.

Ya kuma taɓa zama shugaban Ƙungiyar ƴan kudancin Kaduna (SOKAPU).

Suleiman Othman Hunkuyi - NNPP

Othman Hunkuyi

Asalin hoton, Othman Hunkuyi

Sanata Othman Hunkuyi ne ɗan takarar gwamna ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar NNPP. An haife shi ne a shekarar 1959, ranar 17 ga watan Yuli.

Ya daɗe ana damawa da shi a fagen siyasar jihar Kaduna.

Ya soma yin suna ne a zamanin mulkin tsohon gwamna Ahmed Maƙarfi inda ya riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi.

A 2015 ne ya ci zaɓen zama sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa ƙarƙashin APC amma shi da Sanata Shehu Sani sun fice daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyu bayan da ƴar tsama ta shiga tsakaninsu da gwamna El-Rufai.

Hunkuyi gogaggen ma'aikacin gwamnati ne kuma ya bayyana cewa zai yi amfani da ƙwarewarsa domin inganta rayuwar al'ummar jihar Kaduna idan ya ci zaɓe.

Isa Ashiru - PDP

Isa Ashiru

Asalin hoton, IsaAshiruKudan/Twitter

Isa Mohammed Ashiru shi ne wanda yake yi wa Jam'iyyar PDP mai hamayya takara.

Yana riƙe da sarautar 'Sarkin Bai' a Masarautar Zazzau.

Isa Ashiru, tsohon ɗan majalisar wakilai ne wanda yake neman kujerar gwamna a karo na biyu bayan da ya sha kaye a hannun gwamna El-Rufai a zaɓen 2019.

'Kudan' laƙabi ne da mutane ke kiransa da shi kasancewar ya fito ne daga ƙaramar hukumar kuma ya daɗe a fagen siyasa.

Ya shafe shekara takwas yana ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Kaduna kafin kuma ya samu nasarar zama ɗan majalisar tarayya tsawon shekara takwas.

Shi ma ya kasance daga cikin ƴan takarar da suka halarci muhawarar da BBC Hausa ta shirya inda ya yi magana kan tsare-tsarensa idan ya lashe zaɓe, ciki har da batun inganta lafiya da ilimi.

An haife shi ranar 23 ga watan Oktoban 1962.

Hayatuddeen Lawal Makarfi - PRP

Hayatuddeen Makarfi

Asalin hoton, Hayatuddeen Campaign team

Hayatudden matashin dan siyasa ne mai shekara 37 da haihuwa. Yana daga cikin ‘yan takara mafi karancin shekaru a zaben Najeriya na 2023.

Ya samu digiri a fannin safiyo a jami’ar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Ya yi ayyuka daban-daban a kamfanoni masu zaman kansu.

Sai dai wani aiki da ya fi fito da shi shi ne na Hukumar Ayyukan Gwamnati ta jihar Kaduna (KAPWA) karkashin gwamnatin Nasiru El-Rufai.

Ragowar ƴan takara

Baya ga waɗannan ƴan takara huɗu, sauran da za su fafata a zaɓen na ranar Asabar sun haɗa da:

  • Amb. Sanin Yaya na Jam'iyyar YPP
  • Adamu Abubakar Idris na Jam'iyyar SDP
  • Salihu Abubakar Gambo na Jam'iyyar NRM
  • Andrew Abui Duya na Jam'iyyar APGA
  • Yahaya Alhassan na Jam'iyyar APM
  • Caleb Zagi na Jam'iyyar ADC
  • Yahaya Musa Kallah na Jam'iyyar APP
  • Yusuf Jibril na Jam'iyyar ADP
  • Timothy Sherman Adamu na Jam'iyyar AA