Yadda direbobin motocin kaya suka yi sansani a iyakar Benin da Nijar cikin hotunan Afirka

Mun zaƙulo muku ƙayatattu daga cikin hotunan Afirka na wannan makon.

.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Direbobin motocin dakon kaya sun yi sansani a iyakokin Benin da Nijar ranar Laraba, sakamakon takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara na wasan motsa jiki a jihar Lagos a ranar Litinin.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu daga cikin ɗaliban cibiyar koyarda wasannin motsa jiki wacce Kiyoro Olalekan ya kafa shekaru 30 da suka gabata.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar ƴan Afirka ta Kudu sun yi dandazo a filin jirgin sama na birnin Johannesburg don karɓar baƙuncin ƴan wasan zari-ruga daga kasar Faransa.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Lokacin kaddamar da wasan tseren kekuna a birin Johannesburg ranar Asabar.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a birnin Kigali na ƙasar Ruwanda, yayin taron mako ɗaya na matasan da za su gudanar da gasar wasan ƙwallon kwando daga ƙasashen Afirka 16.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan wasan ƙwallon kwando na Sudan ta Kudu Wenyen Gabriel, kafin fara wasan sada zumunci da kasar Ostireliya a ranar Alhamis a birnin Melbourne.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu noman shinkafa sun ɗauki hoto ranar Laraba a wata fadama kusa da Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar inda sojoji suka hamɓarar da gwamnati.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mata masu goyon bayan juyin mulki a Nijar sun yi dandazo ranar Juma`a, a sansanin sojojin Faransa dake Niamey.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu goyon bayan juyin mulki su na yiwa ƙungiyar ECOWAS da Faransa wacce ta yiwa Nijar mulkin mallaka waƙoƙin zambo, saboda sun yi Allah wadai da hamɓarar da gwamnati.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai Jimar fata a Jihar Kano dake Arewacin Nijeriya.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ya na amfani da hanyoyin gargajiya wajen jeme fata, wacce ake fitarwa ƙasashen ƙetare don yin takalma da jakunkuna da kuma kayan kwalliya na leda.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yara na wasa cikin kwale-kwale a birnin Fass Boye da ke ƙasar Sinigal ranar Alhamis.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani Bafalasɗine ɗan wasan Oud yana waƙa ranar Litinin lokacin bikin al'adu na Carthage a Tunis babban birnin ƙasar Tunisiya.