Me ya sa gwamnatin Kano ke son yi wa gidan Sarki na Nassarawa kwaskwarima?

Asalin hoton, Mai Katanga/Facebook
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nassarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki, tana mai cewa "saboda ya lalace".
Gwamnatin ta kuma umarci kwamishinan 'yansandan jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a ranar Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar.
Kwamashinan Shari'a na Kano, Haruna Isa Dederi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati, inda ya jaddada cewa bangon ƙaramin gidan sarkin da ke ƙwaryar birnin Kano ya "lalace".
"Mun kammala shirye-shirye domin rushewa da kuma sake gina katangar da ta lalace nan take," in ji shi.
To sai dai jama'a na dasa ayar tambaya dangane da dalilin da ya sa gwamnatin ke son aiwatar da gyaran takangar a daidai wannan lokaci?
Me ya sa za a yi kwaskwarimar yanzu?

Asalin hoton, Kamfa
Rahotanni daga Kano na cewa an ga motocin rusau na shawagi a kewayen gidan sarkin na Nassarawa, ƴan sa'o'i bayan sanarwar da gwamnati ta fitar cewa za ta rushe katangar gidan saboda ta tsufa.
Masana harkar sarauta da mulki a Kano da muka tattauna da su da ba sa son a ambaci sunansu sun shaida wa BBC cewa:
"Lallai gwamnati tana da hurumin aiwatar da dukkan wani gyare-gyare da take son yi a wannan gida tunda na masarauta ne kuma ita masarautar nan da ma sarkin duk suna ƙarƙashin ikon gwamnati ne bisa kundin tsarin mulkin Najeriya".
Sannan ma ai gwamnati ce ke naɗa sarki tare da gina gidajensu da fadarsu. Saboda haka ai wannan hurumin gwamnati ne. To amma kuma ai da wuya gwamnati kawai ta ce za ta yi wannan gyara ba tare da masarauta ta nemi yin hakan ba. Ka ga kenan akwai walakin wai goro a miya." In ji wani masanin harkokin sarauta da mulki.
Shi ma wani wanda ba ya son a ambaci sunan nasa ya ce batun gyaran gidan na sarki na Nassarawa ba zai rasa nasaba da kiki-kaka din da ake yi da Aminu Ado Bayero ba.
"Gaskiya gwamnati na da hurumi. To amma abin tambayar a nan shi ne me ya sa ba a yi ba a baya sai yanzu? Ni a fahimtata gwamnati tana son ta rushe katangar gidan ne sai a bar gidan tsirara ka ga kenan Aminu Ado ya zama ga-ni tutsu. Ai ba tsaro kenan. To hakan zai iya tilasta masa barin gidan wanda kuma ita haka gwamnati take so. Tunda ai ta sha bai wa 'yan sanda umarnin su kori Aminu Ado daga gidan." In ji masanin.
Halin da ake ciki a gidan Nassarawa

Wakilin BBC a birnin Kano Zahraddeen Lawan ya je ƙofar gidan Sarkin na Nassarawa da ake taƙaddama a kansa domin ganin abin da ke faruwa.
Sai dai saɓanin yadda rahotanni suka nuna cewa ana shirin ruguje katangar gidan, abin da wakilin namu ya gani shi ne yadda aka jibge jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji a ƙofa da hanyoyin tafiya zuwa gidan.
Zahraddeen Lawan ya ce jami'an tsaron sun rufe hanyoyi da dama da ke zagayen gidan na Nassarawa.

Ina ne Gidan Nassarawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A tarihance gidan Nassarawa ko kuma gidan sarki na Nassarawa kamar yadda aka fi sanin sa a tsakanin Kanawa gida ne da sarkin Kano Abbas kan zauna da Turawan mulkin mallaka a shekarun da ya kwashe yana sarauta watau daga shekarar 1903 zuwa 1919.
Kuma bayan rasuwarsa a 1919 ɗin a gidan aka binne shi. Haka kuma gidan ya ci gaba da zama hubbaren sarukan Kanon. A nan ne aka binne sarki Inuwa da sarki Alhaji Ado Bayero.
Wannan gida dai ya ci gaba da zama wani wurin ganawar sarakuna da baƙi masu muhimmanci. Tsohon sarki marigayi Alhaji Ado Bayero ma a nan yake gana wa da Sarkin Musulmi sannan a gidan ne masaukin Sarkin Musulmin a duk lokacin ya je birnin Kano a zamanin.
Shi ma Muhammadu Sanusi II a zamanin mulkinsa kafin tuɓe shi a 2020, ya kan je gidan a duk ranakun Asabar da Lahadi domin ganawa da baƙi.
Harwayau, shi wannan gida ya kasance wani wurin yada zango ga sarakunan na Kano a lokacin hawan sallah na Nassarawa inda suke yada zango a kan hanyarsu ta zuwa gidan gwamna domin kai gaisuwar sallah.
Me ya sa Aminu Ado Bayero ke zaune a gidan?

Asalin hoton, KAMFA
A ranar 27 ta watan Mayu ne Sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani a Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zaman fada a gidan Sarki da ke Nassarawa.
Wannan dai na zuwa ne sakamakon saɓata juyata da ake samu tsakanin ɓangarensa da na wanda gwamnatin jihar Kano ta ayyana a matsayin sabon sarki, Muhammad Sanusi II, bayan rushe masarautun jihar guda biyar da majalisar dokoki ta yi.
Alhaji Aminu Ado Bayero dai ya koma Kano ne inda ya ce shi ne Sarkin na Kano sakamakon wata takarda da wata babbar kotun tarayya ta fitar tana umartar gwamnatin Kano da ta dakata da matakan da ta ɗauka.
Hukuncin da kotu ta yanke ranar Alhamis
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai bane gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunkuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.
Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi”.
Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.”
Alkalin ya ce tun da har gwamna da kansa ya ce ya samu labarin umurnin kotu, to ya saɓawa doka da ya yi gaban kansa wajen aiwatar da sabuwar dokar masarautun jihar Kano.
“Waɗanda ke kare kansu a shari’ar na sane da umurnin kotun duk da cewa ba a aika musu da kofin umurnin ba. Amma sun gani a kafafen soshiyal midiya, a don haka ba daidai bane su kawar da kai”, in ji Alkali Liman.
Mai shari’a Liman ya mayar da wannan ƙara zuwa wata kotun tarayyar karkashin mai shari’a Amobeda Simon amma har sai an kammala sauraren karar da ɓangaren gwamnati suka ɗaukaka.











