Manchester United na zawarcin de Zerbi, Barcelona za ta ƙulla yarjejeniya da Flick

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta tattauna da tsohon kocin Brighton Roberto de Zerbi kan yiwuwar maye gurbin Erik ten Hag. (Guardian)
Amma wasu rahotanni na cewa United na nazarin ci gaba da kasancewa da Ten Hag a matsayin kocinta. (Manchester Evening News)
Tsohon kocin Bayern Munich da Jamus Hansi Flick zai rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu don zama kocin Barcelona a ranar Laraba. (Fabrizio Romano)
Idan Antonio Conte ya zama sabon kocin Napoli zai nemi ɗaukar ɗan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku mai shekaru 31 domin maye gurbin ɗan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen mai shekaru 25, wanda ke fatan komawa wata ƙungiyar ta Premier League. (Corriere Della Sera)
Paris St-Germain ta shirya fafatawa da Manchester City da Arsenal kan ɗan wasan tsakiyar Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26 wanda ke da farashin £100m (Goal)
Chelsea na tunanin gogayya da Newcastle kan ɗan wasan baya na Ingila Tosin Adarabioyo, mai shekara 26, wanda zai kasance kyauta idan kwantiraginsa da Fulham ya ƙare a wata mai zuwa. (The i)
Leicester na iya zawarcin kocin West Brom Carlos Corberan idan Enzo Maresca ya koma Chelsea. (Talksport)
Manchester United na tsammanin dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 32, zai koma wata ƙungiya ta Saudi Pro League a wannan bazarar kuma a shirye take ta yi babbar asara a kansa. (Football Insider )
AC Milan na zawarcin ɗan wasan Tottenham da Brazil Emerson Royal, mai shekara 25. (Gianluca di Marzio)
Dan wasan tsakiya na Paris St-Germain da Netherlands Xavi Simons, mai shekara 21, na son komawa Barcelona duk da cewa Leipzig da Bayern Munich da Chelsea da Manchester United da Newcastle duk suna sha'awarsa. (Mundo Deportivo)











