Masu buɗe-baki da mutum 800 da aka ɗaura wa aure cikin hotunan Afirka

Ma'aurata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fiye da mutum 800 aka ɗaura wa aure a cocin Pentecostal da ke Kgabalatsane a Afirka ta Kudu ranar Lahadi lokacin bikin Easter
Amariya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata amariya kenan ke cashewa jim-kaɗan bayan ɗaurin auren
Masu azumi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Asabar kenan lokacin da waɗannan musulman suka taru domin cin abinci a lokacin buɗe-baki a Khartoum babban birnin Sudan.
Masu buɗe-baki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Masar ma ɗaruruwan musulmai ne suka taro a Alqahira babban birnin ƙasar domin cin abinci tare a lokacin buɗe-bakin.
Yara

Asalin hoton, GALLO IMAGES

Bayanan hoto, Ɗaruruwan yara ne kuma suka taru a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu a ranar Juma'a a bikin ranar Good Friday.
Masu ɗaukar hoto

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a kenan, lokacin da masu yawon shakatawa ke ɗaukar hoton bakan-gizo a wani tsibiri da ke kan iyakar ƙasashen Zambiya da Zimbabwe