'Abin da ya sa muka tsani baƙi a ƙasarmu'

.
Bayanan hoto, Ƙungiyar ƴan banga ta Operation Dudula

Kungiyar ƴan banga a Afirika ta Kudu mai laƙanin Operation Dudula ta yi ƙaurin suna wajen kai samame a wuraren kasuwancin ƴan kasashen waje tare da rufe shagunansu.

Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya bankaɗo yadda masu cin zarafin baƙi suke cin karensu babu babbaka a ƙasar ta Afrika ta Kudu.

.
Bayanan hoto, Dimakatso Makoena ta ɗora alhakin lalacewar ɗanta kan ƴan ƙasashen waje

Dimakatso Makoena, wata uwa ce mai ƴaƴa uku wadda ke aikin dafa abincin ƴan makaranta a Kwa Thema da ke Gabashin birnin Johannesburg, mai shekaru 57 ta yi wa BBC ƙarin haske ta na zubar hawaye.

"A gaskiya na tsani baƙi, buri na su fice daga ƙasarmu,"

Abu ne mai matuƙar wahala fahimtar dalilin wannan tsananin ƙyamar baƙi, amma lokacin da Miss Makoena ta nuna wa BBC hoton wani yaro a rame ya zazzaro ido kuma jikinsa duk tabon ƙuna sai ta ƙara da cewa:

"Wannan ɗana ne ya fara shaye-shayen kayan maye tun ya na da shekaru 14, yakan fita ya sato kayan mutane don ya sayar ya samu kuɗin sayen kayan maye.

Wata rana ya je satar wayar na'urorin hasken lantarki sai wuta ta kama shi a nan ya samu waɗannan raunukan da suka ɓata masa jiki da fuska.

Ɗanta ya na shan ƙwayoyi irin su crystal meth da nyaope, wasu sinadarai masu tsananin sa maye waɗanda a yanzu matasan da suke ta'ammali da su suka addabi yankuna da dama a fadin ƙasar ta Afrika ta Kudu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Irin wannan yanayi ya sanya iyaye da dama sun goyi bayan ƙungiyar ƴan banga ta Operation Dudula.

An fara ƙaddamar da Operation Dudula ne shekaru biyu da suka gabata a Soweto, ta kasance ƙungiya ta farko da ta fara kai hare-hare kan waɗanda suke haifar da rikicin ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu, wanda ya samo asali tun bayan kawo karshen mulkin ƴan tsirarun farar fata a shekarar 1994.

Ƙungiyar ta fara kiran kanta da sunan ''dudula'' wanda yake nufin kora a harshen Zulu.

Soweto ta kasance a sahun gaba wajen yaƙi da wariyar launin fata a mahaifar Nelson Mandela zaɓaɓɓen shugaban kasar Afirika ta Kudu na farko bisa tafarkin dimokuraɗiyya.

A yanzu garin ya rikiɗe zuwa cibiyar masu ƙyamar baƙi ƴan kasashen waje.

Baƙi na rayuwa cikin fargaba sakamakon barazana daga marasa aikin yi a Afirika ta Kudu, ƙasar da cikin kowanne rukuni na mutane uku ɗaya ba shi da aikin yi.

Adadin baƙi ƴan ƙasashen waje a Afirka ta Kudu bai kai yadda al'ummar ƙasar suke bayyanawa ba idan aka kwatanta da sakamakon binciken da Cibiyar Nazarin Tsaro (ISS) ta fitar a shekara ta 2022.

Rahoton cibiyar ya bayyana cewar akwai aƙalla baƙin haure miliyan 3.95 daidai da kashi 6.5 na al'ummar ƙasar.

Gaba ɗaya adadin da yake daidai da tsarin ka'idojin ƙasa da ƙasa, wannan adadi ya ƙunshi duk wanda ba ɗan asalin ƙasar ba ne ko daga ina ya zo.

Kalaman kyamar baki da wasu jami’an gwamnati da ƴan siyasa da ƙungiyoyin masu kyamar baƙin haure ke amfani da su sun rura wutar jita-jitar cewa ƙasar ta cika da baƙin haure.

Wani binciken ɗabi'un al'ummar Afirika ta Kudu da hukumomin ƙasar suka gudanar a shekara ta 2021 ya gano cewar kusan rabin al'ummar kasar miliyan 60 sun yi imanin cewa baƙin haure tsakanin miliyan 17 zuwa 40 ne suke rayuwa a Afirika ta Kudu.

Wani ƙwarya-ƙwaryan zaɓe ya nunar da cewar jam'iyyar ANC wadda Mandela ya taɓa shugabanta za ta iya samun koma baya da kashi 50 a karon farko.

ƙungiyar ƴan banga ta Operation Dudula ta ɗauki aniyar maye gurbin adadin da ANC za ta rasa, a yanzu ta rikiɗe zuwa jam'iyyar da za ta yi takara a zaɓen da za a gudanar a ƙasar, baɗi.

Shugabar ƙungiyar mai suna Zandile Dabula wadda aka zaɓa a watan Yuni shekara ta 2023 mace ce mai nutsuwa da kwarjini tana sake yin duba game da taken ƙungiyar wanda ke cewa ''bakin haure ne tushen matsalolin tattalin arziƙin Afirika ta Kudu.''

Yayin da aka tambaye ta game da ko yaƙin neman zaben zai karkata kan ƴaki da baƙin haure sai ta shaida wa BBC cewar:

"Ya zama tilas a fahimci cewar dukkan matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan, sun samu ne sakamakon kwararowar baƙin haure da suka yi kama guri zauna.''

"Ƙasarmu ta rushe, ƴan ƙasashen ƙetare sun ƙirƙiri wani tsari na shekaru 20 da nufin su karɓe ikon Afirika ta Kudu.''

Da aka ƙalubalance ta game da wannan batu na karɓe ikon ƙasar sai ta ce jita-jita ce amma ita ta yarda.

"Duk inda ka duba kwayoyin shaye-shaye ne kuma waɗanda suka fi amfani da su al`ummar Afirika ta Kudu ne maimakon ƴan ƙasashen ƙetare, su na shayar da matasanmu ne don su samu sauƙin karɓe ikon ƙasar?''

Tsanar da ake yi wa baƙin hauren ta na ƙarewa ne kan waɗanda suke zaune a ƙasar bisa ƙa`ida.

Wani ɗan Najeriya ya shaidawa BBC yadda ƴan bangar suka ci zarafin sa tare da watsar da kayan kasuwancinsa ba tare da sun tambaye shi komai ba.

"Sai ka koma Najeriya, mu ƴan Afirika ta Kudu ne.'' in ji ayarin ƴan bangar.

Yanzu haka ba shi da sana’a ya na kwana a kan hanya ya bayyana wa BBC cewar : "Na yi zaɓe a ƙasar nan a matsayi na na ɗan ƙasa, ban taɓa ganin ƙasar da ta ke tozarta mutane haka ba, idan na karya doka na cancanci a yi min hukunci ko a mayar da ni ƙasata, amma ban yi laifin komai ba kun ci zarafi na ko kuɗin haya ba zan iya biya ba, abin ya yi yawa zan koma ƙasata.''

Ƙungiyar ta Dudula ta jaddada cewar ta na ayyukanta ne don yaƙi da shigar kayan shaye-shaye to amma babu wata shaida da ta tabbatar da cewar masu sayar da ƙwayoyin ba ƴan Afirka ta Kudu ba ne.

BBC ta haɗu da dakarun na Dadula a Diepkloof da ke Gabashin Soweto lokacin da suke kan hanyar zuwa wurin wani ɗan ƙasar Mozambique bayan wata ƴar Afirika ta Kudu ta kai musu ƙara cewar bai biya ta ƙudin hayar gida ba.

Batu ne da ya kamata a tattauna amma sai Mandla Lenkosi na Kungiyar Dudula ya fara barazanar yi masa duka.

BBC ta tambaye su game da ɗabi’un cin zarafi da sara-suka sai suka amsa cewar su na aiki ne don mutane su bi doka.

Mista Lenkosi, wanda ya fito daga garin Soweto bayan ya rasa aikin yi, na sahun gaba a kungiyar musamman idan sun kai farmaki gidajen baƙin haure ko cibiyoyin da ake zargi ana hada-hadar ƙwayoyi da kuma mutanen da izinin zamansu a ƙasar ya ƙare ba su fita ba.

"Mun girma a lokacin da ƙasar nan ta ke fuskantar wariyar launin fata, amma wancan lokacin ya fi wanan nagarta," In ji dan kungiyar ta Dadula.

Cedric Stone jigo ne a ƙungiyar ta Dudula ya ƙara bayyana wa BBC cewar: "Akwai buƙatar Afirika ta Kudu ta koma lokacin baya.''

"Kakanninmu ne suka fara shagunan cikin motoci amma yanzu ƴan Bangaledesh da Somaliya da Habasha sun karɓe sana’ar, ina dalili?''

Shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya yi Allah-wadai da ƙyamar baƙi da kuma harin da ƴan banga suke kai wa ƴan ƙasashen ƙetare bayan ya danganta irin waɗannan halaye da lokacin wariyar launin fata.

Annie Micheals, wata ƴar fafutuka ce a Johannesburg ta ce ƴan Afirika ta Kudu sun ɗora alhakin yanayin da ake ciki kan waɗanda ba su da laifi, kamata ya yi su gode wa baƙin haure saboda irin jajircewarsu wajen dogaro da kai.

"Ku daina zama wuri ɗaya ku na ƙorafi da jiran gwamnatin da ta gaza wajen biyan buƙatun ku."

Shugabar Ƙungiyar Dadula ta ce waɗanda suke ganin wannan ƙungiya an samar da ita ne don kai hare-hare ba su fahimci ayyukanta ba.

A watan Mayu ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyar sun halarci babban taro a birnin Johannesburg inda mambobi suka kaɗa kuri’ar yin rijista don mayar da ƙungiyar jam`iyyar siyasa.

.
Bayanan hoto, Kungiyar Dadula ta taimaka wa Dimakatso Makoena don rage mata radadi

A lokacin gangamin ƙungiyar, mambobi da magoya baya sun yi dandazo dauke da tutocin Afirika ta Kudu suna rawa da waƙa a kan tituna.

Amma waƙoƙin da suke rerawa na ɗauke da saƙon barazana: ''A ƙone baƙin haure, za mu sayo fetur mu banka wa baƙin haure wuta.''

Kayan Sojoji da suke amfani da su sun yi kamanni da lokacin yaƙi, Miss Makoena na daga cikin masu farin ciki a lokacin gangamin.

Yayin gangamin, Isaac Lesole mai mukamin mai bayar da shawara a ƙungiyar ƴan bangar ta Dudula ya tambayi dandazon magoya baya: "Ku na so mu yi sulhu da baƙin haure?"

"Ba ma so," in ji magoya bayan Dudula.

A tsarin dokokin Afirka ta Kudu yi wa jam`iyya rijista ba ya nufin ta samu damar tsayawa takara akwai wasu sharuɗɗa da za ta bi.

Kungiyar Dudula ba ta da wani tsari ko manufa, sai dai ta na yaɗa manufofinta na matsayarta kan baƙi ƴan ƙasashen ƙetare, kodayake shugabar ƙungiyar Miss Dabula ta ce kungiyar ta na da tasiri a kowanne lardi banda yankin Northern Cape.

Wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyar da suka zanta da BBC sun bayyana bukatar ganin an yi gyara a siyasar ƙasar.

An dora alhakin ƙyamar baƙi a Afirika ta Kudu kan fatara da rashin ayyukan yi da shaye-sharen ƙwayoyi da suka addabi da dama daga cikin al`ummar ƙasar.