Ana zargin gawurtaccen mawaƙi Jay-Z da yi wa yarinya fyaɗe

Jay Z da P Diddy

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Gawurtaccen mawaƙin nan na Amurka, Jay-Z ya mayar da martani a kan zargin da ake yi masa, shi da takwaran aikinsa mawaƙi Sean "Diddy', na banka wa wata yarinya ƴar shekara 13 ƙwaya tare da yi mata fyaɗe a wani taron cashewa a shekarar 2000.

Matar, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta yi zargin cewa lamarin ya faru da ita ne a lokacin wani taron shagali da aka yi a gida bayan kammala taron bayar da kyautukan waƙoƙin da suka ciri tuta na MTV a birnin New York na Amurka.

A cikin wata sanarwa, Jay-Z, wanda sunansa na gaskiya shi ne Shawn Carter, ya yi watsi da zarge-zargen inda ya bayyana su a matsayin ƙoƙarin "ɓata suna".

P. Diddy, wanda ainahin sunansa Sean John Combs – wanda yanzu haka ke a tsare yana jiran shari'a a watan Satumba kan zarge-zargen safarar mata domin lalata da kuma sauran laifuka – shi ma ya yi watsi da zarge-zargen.

A watan Oktoba ne aka fara shigar da ƙarar, inda aka sake shigar da ita a ranar Lahadin nan bayan yi mata wasu gyare-gyare.

Wadda take zargin wadda aka bayyana sunanta kawai a matsayin Jane Doe, ta je wurin cashewar ne a unguwar Manhattan da ke New York lokacin tana da shekara 13 a duniya.

Kamar yadda ta bayyana a ƙarar, lokacin da ta yi ƙoƙarin shiga, ɗaya daga cikin ma'aiktan ta ce "wannan ta yi daidai da abin da Diddy ke nema."

Bayanin ƙarar ya nuna cewa a lokacin da ta isa an buƙace ta ta sanya hannu kan wata takarda, wadda ta yi tunanin cewa batu ne na amincewa kan cewar mutum ba zai bayyana abin da ya faru a wajen ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka nan bayanin ya ƙara da cewa matashiyar ta ga "sanannun mutane" da dama a wurin, sannan ta ga yadda ake ta'ammuli da ƙwayoyi, ciki har da hodar iblis.

A cewar takardar shari'ar, ɗaya daga cikin masu raba abinci a wurin ta ba ta wani lemon kwalba wanda ya sanya ta "jiri", lamarin da ya sanya ta shiga wani ɗaki ta kwanta.

Jim kadan bayan haka ne Jay-Z da Diddy suka shiga ɗakin tare da wata sananniyar mace, waɗanda "ta gane su, su ukun."

A lokacin ne Diddy ya riƙo ta ya ce: "kin shirya cashewa!"

Bayanin ya ƙara da cewa a lokacin ne Jay-Z ya yi mata fyaɗe, yayin da shi ma Diddy ya aikata hakan bayan Jay-Z.

Bayanin ya ƙara da cewa wadda take ƙarar ta samu damar kuɓucewa da ƙyar bayan yunƙurin da ta yi.

Ƙarar na neman a biya matar diyya kan abin da ya faru, tare da bayyana cewa har yanzu tana fama da tsananin damuwa sanadiyyar lamarin.

A cikin sanarwar da ya bayar, Jay-Z, wanda miji ne ga shahararriyar mawaƙiya Beyonce da ƴaƴa uku ya ce ya fi damuwa da tasirin da hakan zai yi ga iyalinsa.